in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gabatar da jawabin taya murnar sabuwar shekara
2015-01-05 13:53:43 cri


A jajibirin bikin sabuwar shekara, shugaban kasar Sin, mista Xi Jin ping, ya gabatar da jawabi na taya murnar sabuwar shekara, ta gidajen rediyon kasar Sin na CRI da CNR, gami da gidan telabijin kasar Sin CCTV.Ga cikakken jawabinsa: 

Lokaci na gudu cikin sauri, yanzu shekarar 2014 ta zo karshenta, yayin da sabuwar shekara ta 2015 ke karatowa. Saboda haka, a wannan lokaci na ban kwana da tsohuwar shekara tare da jiran zuwan wata sabuwa, ina so in nuna fatan alheri ga al'ummomin kasar Sin, da 'yan uwanmu dake yankunan musamman na Hongkong da Macau, da 'yan uwanmu Sinawa dake yankin Taiwan, da wasu kasashen waje, gami da abokai da aminai na kasashe da yankuna daban daban na duniyarmu.

Ma iya cewa shekarar 2014 wata shekara ce da ba a iya mantawa da ita ba, ganin yadda a wannan shekara, muka yi kokarin ingiza matakan gyare-gyare, inda muka wareware wasu matsaloli masu wuya, tare da daukar wasu kwararran matakai, wadanda yawancinsu suka shafi moriyar jama'ar kasar Sin. Mun yi kokarin sabawa da wani sabon yanayin yau da kullum da ake fuskanta a fannin raya tattalin arziki, gami da kokarin neman samun ci gaban tattalin arziki da na zaman al'umma, abin da ya sanya zaman rayuwar jama'a ya kara samun kyautatuwa. Zuwa ranar 12 ga watan Diamba, an kammala matakin farko na aikin kwashe ruwa daga kudancin kasar Sin zuwa arewacin kasar, aikin da ya fara samar da ruwa, lamarin da ya sanya mutane fiye da dubu 400 suka yi kaura domin ba da damar gudanar da aikin. Saboda haka ina so in nuna musu godiya da girmamawa kan yadda suka sadaukar da kansu, tare da fatan za su ji dadin zaman rayuwarsu a sabbin gidajensu.

Duk a wannan shekara, mun yi kokarin daidaita ra'ayoyin jami'ai don tabbatar da da'a, inda muka fi dora muhimmanci kan yaki da daukar matakai marasa amfani, da ra'ayin da wasu jami'an gwamnati suka dauka na ganin kansu a saman farar hula, gami da yadda wasu jami'ai suke son jin dadi da almubazzaranci, ta haka muka samu damar kyautata yanayin da muke ciki. Haka zalika, mun kara kokarin yaki da cin hanci da rashawa, inda muka yanke hukunci mai tsanani ga jami'an gwamnati da suka aikata laifin, abin da ya nuna niyyarmu na kau da cin hanci da rashawa daga kasarmu. Ban da haka kuma, a wannan shekara mun kara yin mu'ammala da hadin gwiwa tare da sauran kasashe daban daban, inda muka karbi bakuncin taron kwarya-kwarya na shugabannin kungiyar hadin kan kasashen Asiya da na tekun Pasific a fannin tattalin arziki (APEC). Har wa yau kuma, shugabannin kasarmu sun ziyarci kasashe da yawa, yayin da shugabannin kasashe daban daban su ma sun kawo ziyara a nan kasar Sin. Duk wadannan ayyuka sun sa jama'ar kasashen duniya suka samu damar kara sanin kasar Sin.

Don aiwatar da wadannan ayyuka yadda ya kamata, jami'an gwamnatinmu na matakai daban daban sun yi aikin tukuru. Sai dai ba abu ne mai yiwuwa a kammala wadannan ayyuka ba, in ba tare da samun goyon baya daga jama'ar kasarmu ba. Saboda haka ina so in yaba ma jama'armu da nuna musu godiya.

A shekarar 2014, mun zartas da wasu dokoki don tabbatar da ranakun tunawa da samun nasara a yakin kin harin Japan, da tunawa da wadanda suka sadaukar da rayukansu don kare kasar, da tunawa da wadanda suka rasa rayuka a kisan kiyashin da sojojin Japan suka yi a birnin Nanjing, daga baya mun shirya gagaruman bukukuwa a duk wadannan ranaku masu muhimmanci. Game da mutanen da suka sadaukar da rayukansu domin kare kasa da al'umma, ko kuma domin kare zaman lafiya, ba za mu manta da yadda suka sadaukar da kai da gudunmowar da suka samar ba har abada, duk wata canzawar zamani da ta abku.

Duk a shekarar 2014, mun gamu da wasu al'amuran da suka bakanta rai sosai. Ga misali, jirgin sama mai lambar MH370 na kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Malaysia da ya dauki 'yan uwanmu Sinawa fiye da 150 ya bace. Har yanzu ba mu taba mantuwa da su ba, kuma za mu ci gaba da kokarin neman samunsu. Ban da haka kuma, a wannan shekara mun gamu da wasu bala'o'i daga indallahi da wasu hadaruruka, wadanda suka haddasa rasa rayuka sosai. In ba ku manta ba, bala'in girgizar kasa da ta abku a gundumar Ludian ta lardin Yunnan ita kadai ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 600. Muna begen wadanda suka rasu, da fatan iyalansu za su kasance cikin koshin lafiya.

Yanzu ana shirin kada kararrawar maraba da sabuwar shekara, a wannan lokaci mun yi niyyar ci gaba da kokarin aiki, don daukar matakan da jama'a suke fatan gani, da mai da burinsu ya zama abin gaskiya. Za mu ci gaba da zurfafa gyare-gyaren da muke dauka daga dukkan fannoni, domin kibiyar da aka harba ba za ta juya baya ba, kana gyare-gyaren da ake yi na bukatar jan hali da kwarin gwiwa. Za mu aiwatar da manufar kula da harkokin kasar bisa dokoki, ta yadda za mu samu damar kare hakkin jama'a, da tabbatar da adalci da daidaituwa a zaman al'umma, da raya kasarmu, bisa yin amfani da dokoki. Za mu sanya zurfafa gyare-gyare da kula da harkokin kasa bisa dokoki su zama manufofi 2 masu muhimmanci dake taimakawa kokarin cimma burinmu na kafa wani zaman al'umma mai walwala.

Yanzu zaman rayuwar jama'ar kasarmu na ta samun kyautatuwa, amma ya kamata mu lura da mutanen da suka gamu da matsaloli a zaman rayuwarsu a ko da yaushe. Kamata ya yi mu nuna himma da kwazo a kokarin kula da aikin da ya shafi zaman rayuwar jama'a, musamman ma a fannonin tallafawa matalauta da ba da tabbaci ga ingancin zaman rayuwarsu, ta yadda za mu sanya masu fama da talauci dake kauyuka da birane, da duk wanda yake da bukata, su samu damar magance jin yunwa, da samun gamsuwa a zukatansu.

Ban da wannan kuma, ya kamata mu ci gaba da sa ido kan 'yan jam'iyyarmu ta Kwaminis ta kasar Sin bisa doka yadda ya kamata, da tsayawa kan kokarinmu na daidaita al'adarmu ta fuskar aiki. Za mu nace ga kokarin yaki da cin hanci da rashawa, da kara kyautata tsare-tsarenmu a wannan fanni, domin a wannan kasa dake bin tsarin gurguzu a karkarin jagorancin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ba za a yi hakuri da danyen aiki na cin hanci da rashawa ba. Duk wanda ya aikata wannan laifi, to, za a yanke masa hukunci.

Aikin da muke gudanar da shi wani babban aiki ne mai muhimmanci, wanda sai mutane masu hakuri da jan hali ne za su iya cimma nasarar aiwatar da shi. Bai kamata ba wani ya yi azumin shekara, ya kurkure da tafannuwa. Tun da muna da wani babban buri, tabbas ne za mu gamu da wuya a kokarin cimma wannan buri. Saboda haka, ina kira ga jama'armu na kabilu daban daban da su yi tsintsiya madaurinki daya, da kokarin tara shawarwari masu kyau, ta yadda za a samu damar yin amfani da damar da muke da ita, da daidaita matsalolin da muka gamu da su yayin da muke tinkarar kalubale, tare da kirkiro wasu sabbin fasahohi, domin raya kasarmu tare da kyautata zaman rayuwar jama'armu.

A nasu bangaren, jama'ar kasar Sin suna mai da hankali kan makomar kasarsu, yayin da a sa'i daya suke sa lura ga yanayin da duniya za ta kasance ciki a nan gaba. Saboda haka jama'ar kasar Sin sun taba samar da nasu tallafi da gudunmowa ne yayin da annobar cutar Ebola ta barke a nahiyar Afirka, kuma yayin da aka fama da karancin ruwa a fadar mulkin kasar Maldives. Wadannan matakai da aka dauka sun sheda yadda jama'ar kasar Sin suke zama kafada da kafada da jama'ar kasashe daban daban yayin da suke fuskantar matsaloli.

Yanzu yanayin duniyarmu ba shi da natsuwa, don haka muna kira da a kiyaye zaman lafiya. Muna fatan jama'ar kasashe daban daban za su yi kokari tare, don fitar da dukkan mutane daga kangin talauci da yunwa, da sanya dukkan iyalai su kauracewa wutar yaki, da tabbatar da ganin dukkan yara za su girma cikin wani yanayi na zaman jituwa da kwanciyar hankali.

Na gode kwarai da gaske.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China