in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya kafa sabon yanayin diplomasiyya a kasar Sin
2014-10-11 21:35:08 cri

Tun bayan da aka rantsar da sabbin shugabannin kasar Sin shekaru 2 da suka gabata, shugaba Xi Jinping na kasar ya kai ziyarce-ziyarce kasashen waje har sau 10. Ra'ayinsa da matakai na daidaita harkokin waje da yake dauka sun jawo hankulan duniya kwarai a kai a kai. Mr. Qu Xing, direktan hukumar nazarin harkokin kasa da kasa ta kasar Sin ya bayyana cewa, shugaba Xi ya fi mai da hankali kan huldar dake tsakanin manyan kasashen duniya, da kasashen da suke makwabtaka da kasar Sin, da kuma yadda za a karfafa huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashe masu tasowa. Bugu da kari, yana kokari kwarai kan yadda za a iya daidaita batutuwan dake jawo hankulan jama'a sosai.

Mr. Qu Xing ya shaidawa wakilinmu cewa, shugaba Xi yana da sabbin ra'ayoyin diplomasiyya. Alal misali, game da batun raya huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, Mr. Xi ya bullo da ka'idoji 4 da ke kunshe da kalmomi 4, wato "Gaskiya, kirki, alheri, sahihanci". Sannan, yana ganin cewa, kasar Sin da kasashen Afirka sun kasance kamar wata kungiyar dake da fata iri daya.

Bugu da kari, Qu Xing yana ganin cewa, shugaba Xi Jinping ya fi mai da hankali wajen tsara babbar manufar daidaita harkokin diplomasiyya. Lokacin da yake tsai da kuduri kan harkokin diplomasiyya, ya fi mai da hankali kan babbar ka'idar da dole ne a bi, wato ya kan mai da hankali kan lamari mafi muni da mai yiyuwa ne zai faru.

Mr. Qu Xing ya bayyana cewa, wadannan ka'idoji da tunani sun ba da gudummawa sosai kan ci gaban harkokin diflomasiyyar kasar ta Sin, sun samar da hanyoyi daban daban da suka dace wajen warware sabanin da ke tsakanin kasashe, ta yadda kasar Sin ta sami dama masu kyau wajen neman bunkasuwarta. Ya kuma ba da misali cewa, a halin yanzu, dangantakar dake tsakanin manyan kasashe na da sarkakiya, kamar dangantakar dake tsakanin kasar Amurka da kasar Rasha, kasar Rasha da kungiyar tarayyar kasashen Turai da kuma dangantakar dake tsakanin kungiyar EU da kasar Amurka da dai sauransu, amma bisa akidar kasar Sin kan bunkasa dangantakar dake tsakaninta da manyan kasashe, ya kamata a nuna hadin gwiwa cikin himma da kwazo. Kasar Sin na dukufa wajen magance abkuwar rikici irin na manyan kasashe a tsakaninta da kasar Amurka, haka kuma, kasar Sin da kungiyar EU sun riga sun kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai wasu kasashen Turai a farkon rabin shekarar bana ta sami nasara sosai, inda a karo na farko ya ziyarci hedkwatar kungiyar EU, da kasashe guda hudu wadanda suka kafa kungiyar EU da kuma kasashe guda biyu wadanda suka samu saurin bunkasuwar tattalin arziki. A halin yanzu, ana bunkasa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai cikin yanayi mai kyau. A sa'i daya kuma, kasar Sin da kasar Rasha sun kafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare. Lamarin da ya sa, ana ganin cewa, shugaba Xi Jinping ya cimma nasarori da dama wajen kyautata dangantakar dake tsakanin kasar Sin da wasu manyan kasashe.

Wannan ya taimaka wajen sabunta hanyoyin bunkasuwar harkokin diflomasiyya yadda ya kamata.

Tunanin shugaba Xi Jinping kan harkokin diflomasiyya ya dace da halin da ake ciki sosai. Mr. Qu ya ce, a watan Yuli da na Agustan shekarar bana, shugaba Xi ya kai ziyara a kasashen Koriya ta Kudu da Mongolia bi da bi, lamarin ya nuna ci gaban kasar Sin kan bunkasa dangantakar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, ya kuma nuna tunanin shugaba Xi wajen kiyaye dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen da ke makwabtaka da ita, ya kuma dace da yadda ake bunkasa harkokin diflomasiyyar kasa ta Sin yadda ya kamata.

Mista Qu ya kara da cewa, kasar Sin ba ta sauya manufarta ta diplomasiyya kan kasashe makwabta ba, ta kyautata da inganta manufarta ta kulla hakkin makwabtaka da abokantaka da wadannan kasashe. Alal misali, kasar Sin na kokarin raya kanta tare da kawo wa kasashen da ke makwabtaka da ita alheri, a maimakon zaman lafiya tare da su kawai. Haka kuma kasar Sin tana kokarin nuna sahihiyar zuciya kan mabambantan hanyoyin mulkin kasa, da mabambantan ra'ayoyi a harkokin duniya, da kuma tsare-tsaren zaman al'ummar kasa iri daban daban, yayin da take samun saurin bunkasuwa da kara samun karfi tare da kara samun tasiri, yayin da kasashen duniya suke kara mai da hankali kan kasar Sin.

A lokacin da shugaba Xi yake ziyara a wasu kasashe, ya yi bayani sau da dama kan muhimmancin kafofin yada labaru na wurin. A ganin mista Qu, ko wane bayanin da shugaba Xi ya rubuta ya kan mai da hankali kan kyakkyawar huldar da ke tsakanin Sin da wadannan kasashe, bisa abubuwan da jama'ar wurin suka mai da hankali a kai, da abubuwan da suka kusance iri daya a tsakanin Sin da wadannan kasashe ta fuskar al'adu, da kuma mu'amalar da ke tsakanin Sin da wadannan kasashe a tarihi, lamarin da ya kasance tamkar wata sabuwar hanyar kulla huldar diplomasiyya a tsakanin al'umma a sabon zamanin da muke ciki.

Mista Qu ya ci gaba da cewa, a baya kasar Sin ba ta dora muhimmanci kan yayata kanta ba. Amma yanzu lokaci ya wuce, idan ba ta kara yayata kanta ta hanyar da ta dace ga kasashen duniya ba, watakila ba za ta iya bayyana muhimman bayanan da ke fatan sani ba, don haka jama'ar kasa da kasa ba za su iya fahimtar kasar Sin cikin sauki ba. Bayanan da shugaba Xi ya yi kan muhimmancin kafofin yada labaru na kasashen da yake ziyara tare da sanya ambaton sunayen su, ya haifar da sakamako mai kyau a fannin kulla huldar diplomassiya a tsakanin al'umma. (Sanusi Chen, Tasallah, Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China