in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane fiye da dubu 90 sun rasa gidajensu a sakamakon rikicin da ya abku a yammacin kasar Iraki
2015-04-20 14:49:39 cri

Tawagar wakilan MDD masu taimakawa kasar Iraki ta bayar da sanarwa dake cewa, mutane fiye da dubu 90 sun rasa gidajensu, a sakamakon rikicin da ya abku a jihar Al-Anbar dake yammacin kasar Iraki, kana wadanda suka tsira bayan aukuwar tashin hankali a jihar na matukar bukatar tallafin jin kai.

Sanarwar ta ce, iyalai fiye da dubu 10 dake zaune a birnin Ramadi, helkwatar jihar Al-Anbar sun yi kaura zuwa gabashin jihar da birnin Bagadaza, da sauran yankunan dake kewayen birnin, sakamakon tsanantar tashin hankali a yankin.

Jami'i mai kula da harkokin jin kai na MDD dake kasar Iraki Lise Grande, ya fidda wata sanarwa dake cewa hukumomin jin kai suna iyakacin gaggauta kokarinsu wajen taimakawa wadanda suka tserewa gidajensu, inda ake dora muhimmanci ga samar musu abinci, da ruwan sha, da wuraren kwana da sauran muhimman kayayyakin masarufi na yau da kullum.

Sai dai a daya hannun Lise Grande ya ce, tallafin jin kai da ake samarwa, ba zai iya biyan bukatun dukkanin mutane ba. Duba da cewa kusan kashi 60 cikin dari na yawan kayayyakin taimako, wadanda sassan masu aikin jin kai suka samar za su kare, idan har ba a samu karin kudaden taimako a kan lokaci ba. Don haka ne kuma ya yi kira ga hukumomi, da mawadata, da su samar da karin kudaden taimakon jin kai. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China