in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Iraki ya yi kira ga kasashen duniya da su kara goyon bayan yaki da kungiyar IS
2015-04-14 11:20:24 cri

A jiya Litinin, firaminsitan kasar Iraki Haider al-Abad ya bayyana fatan sa ga kasashen duniya na su kara taimakawa wajen yaki da kungiyar IS.

Haider al-Abad ya bayyana hakan ne jim kadan kafin ya tashi zuwa Washington DC na kasar Amurka a wannan rana domin kai ziyararsa ta farko tun bayan da ya zama firaministan kasar Iraki.

Ya bayyana cewa kasar Iraki ta samu wasu nasarori wajen yaki da kungiya mai tsattsauran ra'ayi ta IS, amma tana ci gaba da fuskantar babban kalubale yayin da take kokarin komar da jihar Al-Anbar dake yammacin kasar da kuma birnin Mosul dake arewacin kasar a hannun gwamnati, don haka yana fatan kasashen duniya za su kara goyon bayan kasar da daukar matakai don hana karin dakaru su shiga cikin kasar Iraki.

Haider al-Abad ya ce, yana fatan ziyararsa za ta ciyar da huldar kasashen Iraki da Amurka gaba, kana za su cimma matsaya daya kan fannonin kiyaye ikon mulkin kasa da kare moriya iri bai daya na kasashen biyu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China