Mashirya taron shekara-shekara na kamfanonin kasar Sin dake kasar Afirka ta Kudu ne suka bayyana hakan a jiya Alhamis. An ce yawan kudaden cinikayyar sassan biyu a shekarar 2014 da ta gabata, ya kai dalar Amurka biliyan 60 da miliyan dari 3, wanda hakan ya sanya Afirka ta Kudu kasance kasa mafi yawan cinikayya tare da kasar Sin a nahiyar Afirka cikin shekaru 5 a jere, kana kasar Sin ta kasance kasa mafi yawan cinikayya tare da Afirka ta Kudu, da kasuwa mafi girma ta fitarwa ko shigar da kayayyaki a duniya cikin shekaru 6 a jere.
Taron wanda ya gudana a birnin Pretoria, ya samu halartar wakilai 150 daga kamfanonin Sin, da hukumomi, da kafofin watsa labaru na Sin fiye da 80.
Cikin jawabin da ya gabatar, jakadan Sin a kasar Afirka ta Kudun Tian Xuejun, ya yabi muhimmin ci gaban da aka samu a shekarar da ta gabata, a fannin dangantakar tattalin arziki, da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu, ya kuma yi nuni da cewa, farfadowar tattalin arzikin duniya, da kyautatuwar tsarin tattalin arzikin Sin da Afirka ta Kudu, na kara samun ci gaba, bisa hadin gwiwar tattalin arziki, da cinikayya a tsakanin kasashen biyu. Kana jakada Tian ya yi fatan kamfanonin Sin dake kasar Afirka ta Kudu, za su rungumi ra'ayin cimma moriya mai dacewa, da kokari wajen samun moriyar juna, da kara yin hadin gwiwa a manyan fannoni, da gudanar da ayyukan daga matsayin hadin gwiwa tsakanin su da kasashen Afirka zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)