Har kullum Sin na tsayawa tsayin daka kan cewa, kamata ya yi kasashen da ke shafar batutuwan teku, su warware rikici kai tsaye ta hanyoyin yin shawarwari da tattaunawa. Kazalika kasar na fatan wasu kasashe za su kara gudanar da ayyukan da za su yi wa yankin amfani, in ji Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin yau Jumma'a 17 ga wata a nan Beijing.
An fidda wata sanarwa a yayin taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G7, wadda ke nuna bukatar daukar matakan bai daya, game da yunkurin sauya halin da ake ciki yanzu haka a yankunan tekun Gabas da tekun Kudu, da kuma batun tsanantar halin ja-in-ja da ake ciki a yankin.
Sanarwa wadda aka fitar a ranar Laraba, ta kuma goyi bayan kafa tsarin yin hadin gwiwa a yankin ta fuskar tsaron teku, tare da jaddada muhimmancin matakan karfafa amincewa da juna, wadanda aka dauka a yayin taron tattaunawa tsakanin kasar Sin da kungiyar hadin kan kasashen Kudu maso Gabashin Asiya ko ASEAN, dangane da ka'idojin ayyukan kan tekun Kudu.
Dangane da wannan lamari, Hong Lei, ya bayyana wa taron manema labaru da aka saba shiryawa cewa, kasar Sin ba ta taba sauya matsayinta kan batun tekun Kudu ba. Ya ce, har kullum Sin tana himmantuwa wajen gama kai da kasashe masu ruwa da tsaki, kan kiyaye zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da kuma kara azama kan hadin gwiwar moriyar juna a yankin. Yanzu haka dai ana cikin kwanciyar hankali a yankin, inda ake hada kai yadda ya kamata a wasu fannoni. (Tasallah Yuan)