A gun taron jami'an Sin da na sauran kasashen kungiyar ta ASEAN sun bayyana cewa, babu wata kasa da ke goyon bayan manufar dakatar da ayyuka a tekun kudancin kasar Sin wanda kasar Amurka ta gabatar.
Jami'an sun bayyana cewa, yayin taron ministocin harkokin wajen kasashe kungiyar ASEAN, wasu kasashe sun bayyana tabarbarewar dangantaka tsakanin Sin da wasu kasashe mambobin kungiyar ASEAN, duk kuwa da cewa wannan batu ne da ba shi da tushe bare makama. Hasali ma dai kasar Sin da kungiyar ASEAN, sun amince da batutuwan dake kunshe cikin sanarwar da aka fitar, wadda ta dace da ra'ayoyinsu da aka cimma a baya. Koda yake wasu kasashe sun sauya hakan da gangan, lamarin da ya nuna cewa, ba sa kan gaskiya game da wannan batu. (Zainab)