in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Brazil za ta kwaikwayi tsarin da Jamus ta bi wajen horas da matasan 'yan wasan kwallo
2015-04-16 15:17:54 cri
Kamar dai yadda masu salun-magana kan ce "Fadan da yafi karfin ka sai ka maida shi wasa". A yanzu haka dai hukumar kwallon kafa ta kasar Brazil, ta ce ya zama dole ta yi koyi da tsarin da Jamus ta bi wajen samar wa kan ta matasan 'yan wasa masu nagarta, bayan da Jamus din ta lallasa Brazil da ci 7 da 1. A wasan kusa da kusan na karshe da suka buga cikin watan Yulin bara, a gasar cin kofin duniya da Brazil din ta karbi bakunci.

Wasu kafofin yada labarun kasar ta Brazil sun rawaito hukumar wasan kwallon kafar Brazil CBF, na cewa ta na shirin koyi da tsarin na Jamus, domin ceto kai daga halin dirkushewa a fannin taka-leda.

Jamus dai ta kulla wata wangila da wasu kwararru daga Belgian, wadanda su ke samar wa kasar dabarun sauya tsarin kwallon kafa, ta yadda kasar za ta ci gaba da gogayya da sauran kasashen duniya.

Karkashin shirin, tawagar kwararrun mai suna "Double Pass" ta na gudanar da nazari a ko wace shekara kan tawagogin matasa 'yan wasan kasar, wadanda ke koyon kwallo a rukunoni biyu mafiya kwarewa.

An ce kwararrun na duba sassan abubuwan bukata domin horas da 'yan wasa, da fannin horaswa, da fannin sadarwa. Sauran sassan sun hada da na hadin gwiwa da sauran hukumomi, da harkokin gudanarwa, da sadarwa, da na tsare-tsare da kuma na samar da kudade.

Daga nan kuma kwararrun sai su mika sakamakon binciken na su zuwa hukumar kwallon kafar kasar ta Jamus, wadda ke jera kulaflikan kasar gwargwadon matsayin su na kwarewa bisa sakamakon nazarin.

Jamus dai ta kirkiri wannan dabara ne a shekarar 2007, wanda hakan ya yi matukar kara yawan masu horas da 'yan wasan kasar, da bunkasa filayen wasa, da kayan horas da 'yan wasan, tare kuma da samar da managarcin tsarin sarrafa kudade. Baya ga babban batu, na samun nasara a fagen gasanni.

A halin yanzu dai karkashin hukumar CBF, Brazil na lura da nasarar horas da matasan 'yan wasa a kulaflikan Atletico Mineiro, da Santos, da kuma Sao Paulo. Inda ake ganin matakin ya taimaka wajen samar ababen bukata na horo, da kudaden da ake bukata wajen daukar nauyin 'yan wasa.

Wannan mataki dai ya dace da manufar sabon shugaban hukumar ta CBF Marco Polo Del Nero, wanda zai maye gurbi shugaban hukumar mai barin gado Jose Maria Marin a ranar Alhamis 16 ga watan nan. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China