in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban hukumar wasan kwallon kafar Ghana zai shiga tsakani a rikicin da ya dabaibaye harkar kwallon kafar Kenya
2015-03-26 14:25:10 cri
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta nada shugaban hukumar kwallon kafar kasar Ghana Kwesi Nyantakyi, a matsayin wakili mai shiga tsakani, don gane da rikicin da ya dabaibaye harkar kwallon kafar kasar Kenya.

A cewar kakakin hukumar kwallon kafar kasar Ghana Ibrahim Saanie Daara, Nyantakyi zai jagoranci tawagar mutane 3, wadanda ake fatan zasu tattauna da bangarori daban daban, da nufin warware matsalar da harkar kwallon kafar kasar Kenya ke fuskanta.

Sauran mambobin tawagar sun hada da Ashford Mamelodi, jami'in bunkasa harkokin wasanni na hukumar ta FIFA, da kuma Primo Carvaro, mamba a majalissar hukumomin FIFAr.

Rahotanni dai na nuna cewa manyan kulaflikan kwallon kafar kasar ta Kenya sun tsunduma cikin wani rikici ne, biyowa bayan Baraka da aka samu, wadda ta sanya bangarori biyu na kulaflikan kasar, fara buga wasannin kalubale na kasar kashi biyu a lokaci guda.

A yanzu haka dai gasar zakarun kulaflikan kasar ta KPL na da kulaflika 16 da ke fafatawa a cikin ta, kana masu shirya gasar sun ki amincewa a fadada ta zuwa kulaflika 18, kamar yadda babbar hukumar gudanarwar kwallon kafar kasar FKF ta bukata.

Wannan dai kiki-kaka shi ya janyo sassan biyu fara buga gasanni biyu dake kunshe da kungiyoyi iri daya, yayin da masu sha'awar kwallon kafar kasar ke ganin mai yiwuwa ne, a tursasawa kulaflikan zabar daya daga gasannin biyu, saboda yawan wasannin da za su buga idan har suka ci gaba da buga duka gasannin.

A daya hannun kuma, akwai matsalar filayen wasan da ake amfani da su a gasannin biyu da bangarorin biyu ke gudanarwa.

Hukumar FIFA dai na fatan tura tawagar sasantawar za ta taimaka wajen warware matsalar da ake fama da ita a Kenya.

Ba dai wannan ne karo na farko da aka samu irin wannan matsala ba a kasar, domin kuwa rahotanni sun nuna cewa yayin kakar wasanni ta 2005-2006, an taba samun rashin jituwa tsakanin masu fada a ji a harkar kwallon kafar kasar, lamarin da a wancan lokaci ma ya haddasa rabuwar kawuna gida biyu kamar dai irin na wannan lokacin. Kafin daga bisani gwamnatin kasar ta rushe hukumar harkokin kwallon kafar kasar baki daya, a kuma samu nasarar warware takaddamar ta wancan lokaci.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China