Labarin ya bayyana cewa, a lokacin saye da musayar 'yan wasa na kakar 2014-2015, Sin ta zuba jari da kudin Brazil Real miliyan 119, don sayen 'yan wasan kwallon kafa 6 daga kasar. Wadannan 'yan wasa da Sin ta saya dukkansu su 'yan wasa ne masu kyau a kasar, don haka kudin da aka saye su ya ke da yawa.
Kafofin watsa labaru na kasar Brazil sun bayyana cewa, duk da yake shekarun da Sin ta kwashe ta na gudanar da gasar kwallon kafa bas u da yawa, a hannu guda kasar ta riga ta hau matsayi na 9 wajen daddale yarjejeniyar sayen 'yan wasan kwallon kafa a duniya. A wadannan shekaru, Sin ta kara yawan jarin ta wajen sayen 'yan wasa daga kasar Brazil.
A kakar 2010-2011, ta kashe kudin Brazil Real miliyan 15.4 don sayen 'yan wasan Brazil, matakin da ya kasance kasa da na takwas a duniya a wannan fanni, yayin da a shekarar bara ta kasance kasa ta uku.(Zainab)