Ceni dan shekaru 42, ya ciwa kulaf din na sa kwallo ta 127 a ranar Asabar din karshen makon jiya, ta bugun daga kai sai mai tsaron gida. Matakin da wasu masu nazarin harkokin kwallon kafa ke kallo a matsayin muhimmiyar nasara gare shi, irin wadda ba a saba gani a kulaflikan turai ba.
A jeren masu tsaron gida da suka ciwa kulaflikan su kwallaye da dama dai Ceni ne ke kan gaba, yayin da mai tsaron gidan Paraguay Luis Chilavert, wanda yayi ritaya a shekarar 2004, ke biye a matsayi na 2 da kwallaye 62.
Ceni, ya tara rabin yawan kwallayen sa ne ta bugun free-kick, yayin da kuma rabin ya zura su a raga ta bugun daga-kai-sai-mai tsaron gida.(Saminu Alhassan)