in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FC Porto ta samu nasara kan Arouca 1-0 a ci gaba da gasar kwallon kafar kasar Portugal
2015-03-18 10:25:51 cri
Kulaf din FC Porto na kasar Portugal ya samu nasara kan takwaransa na Arouca da ci 1 da nema, a wasan sati na 25 da suka buga a filin wasa na Dragao.

Yanzu haka dai FC Porton ce ke matsayi na 3 a teburin gasar kalubale ta kasar Portugal da maki 61, inda take biyewa Sporting CP mai maki 67. A can saman teburin kuwa Benfica ce ke matsayi na daya da maki 74, yayin da kulaf din Arouca ya sauka zuwa matsayi na 12 da maki 31.

A ragowar wasannin ranar Lahadin da ta gabata, kungiyar Moreirense ta doke Gil Vicente da ci 1 da nema, sai Academica wadda ta samu nasara kan Nacional da ci 2 da 1. Sauran wasannin su ne wasan da Rio Ave ta doke Penafiel da ci 2 da nema, yayin da Sporting Braga ta jefawa Maritimo kwallo daya mai ban haushi.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China