in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bata gari sun ci gaba da tada hankula yayin wasannin kwallon kafar kasar Greece
2015-03-12 14:42:29 cri
Rahotanni daga kasar Greece na cewa magoya bayan kulaflikan kwallon kafar kasar sun ci gaba da tada hargitsi, yayin wasannin "Super League" na kasar, matakin da ya tilasawa hukumar gudanar da gasar hana 'yan kallo shiga kallon wasannin da aka buga a karshen makon jiya.

Makwannin biyu da suka shude ma sai da ministan wasannin kasar ya bada umarnin dage wasanni tsahon mako guda, biyowa bayan hargitsin da bata kari dake goyon bayan kulaflikan kasar biyu suka tayar, ya yin wasanni biyu cikin watanni 6.

Sai dai duk da hana 'yan kallo shiga filin wasan da aka yi, an ce magoya bayan kulaflikan PAOK da Aris, sun kwabza fada a wajen ofishin daya daga cikin kulaflikan dake birnin Thessaloniki a Arewacin kasar ta Greece.

Rahotanni sun ce daya daga cikin 'yan kallon ya samu mummunan rauni.

A baya ma gabanin lokacin sanyi da ya shude, wani magoyin bayan daya daga kulaflikan kasar ya rasa ransa a irin wannan hargitsi a tsibirin Crete.

Kafin dakatar da shiga kallon wasan na wannan karo, a baya ma an taba sanya wannan doka, lokacin da aka raunata wani alkalin wasa a irin wannan tashin hankali da 'yan kallo ke tayarwa a kasar ta Greece.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China