in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu horsa da manyan kulaflikan kasar Sifaniya na burin samun karin nasarori
2015-03-26 10:56:00 cri
Kocin FC Barcelona Luis Enrique ya ce da-sauran-rina-a-kaba, game da matsayin kulaf din a gasar La liga da suke bugawa, duk kuwa da nasarar doke Real Madrid 2-1 da suka yi a gida, matakin da ya baiwa kulaf din na sa damar baiwa Real Madrid din tazarar maki hudu a teburin gasar.

Luis Enrique ya ce ba ya sha'awar zuzuta nasara, ko sakamakon da yake samu, musamman a wannan lokaci da ya rage wasanni 10 su kammala buga gasar La ligan ta bana.

Ya ce cikin wadannan wasanni 10 akwai maki 30 da za a iya samu, duk da cewa su na matsayin da muke fata, wasan su na gaba da Celta ba wasa ne mai sauki ba.

Duk da wannan taka-tsantsan, Enrique ya bayyana farin ciki game da nasarar da suka samu, kan kulaf din dake matukar adawa da su, musamman ma bayan samun nasarar doke Manchester City da suka yi a 'yan kwanakin baya.

A daya hannun kuma kocin Real Madrid Carlo Ancelotti, na ganin kulaf din sa ya taka leda yadda ya kamata, sai dai 'yan wasan sa sun gaza cin kwallaye tun a zangon farko na wasan.

Ancelotti ya kara da cewa kulaf din sa ya taka rawar gani, duk da matsayi na biyu da yake a yanzu bayan Barca, matsayin da ya ce yana da wuya gare su. Ya ce duk da hakan ba zasu karaya ba, za su ci gaba da kwazon ganin sun lashe gasar ta La liga. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China