in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dalilin da ya sa Marcello Lippi ya bar Evergrande
2015-03-18 10:30:44 cri

Marcello Lippi shahararren mai horar da 'yan wasan kwallon kafa ne dan asalin kasar Italiya, wanda ya fara jagorantar kulob din kwallon kafa na Evergrande dake nan kasar Sin tun daga shekarar 2012.

Sai dai a watan da ya gabata, babban kocin ya yi murabus daga mukaminsa, ya koma kasarsa Italiya, lamarin da ya sanya aka rika cece-kuce game da dalilin barinsa kulob din na Evergrande tun kafin cikar wa'adin aikinsa.

Wasu dai na ganin rashin kyakkyawar dangantaka tsakanin Lippi da shugabannin kulob din na Evergrande ne ya janyo hakan. Musamman ma kasancewar Lippi shahararren koci, wanda a duk kulob din da yake, yana son zama mai fada a ji. Hakan ya sa wani lokaci ake samun bambancin ra'ayi tsakanin Lippi da masu kulob din na Evergrande.

Ga misali, a yayin gasar cin kofin CSC da ta gudana a bara, Lippi ya ki tura kwararrun 'yan wasa domin halartar gasar, maimakon haka ya tura wasu 'yan wasa matasa, sakamakon rashin amincewarsa da tsarin gasar, musamman ma a fannin lokacin gudanar ta. Haka zalika, yayin bikin ba da lambar yabo da ya gudana a kakar wasanni da ta wuce, mista Lippi ya ki zuwa birnin Beijing domin halartar bikin, duk da cewa yana cikin kasar Sin a lokacin, abin da ya raunana huldar dake tsakanin kulob din na Evergrande da hukumar wasan kwallon kafar kasar Sin.

Amma rikici mafi tsanani da ya auku tsakanin mista Lippi da kulob din Evergrande shi ne na dakko 'yan wasa daga ketare, inda shi Lippin ya shigo da 'yan wasan Italiya 2, wato Alessandro Diamanti da Alberto Gilardino, wadanda dukkansu suka kasa taka rawar a-zo-a-gani a kulob din na Evergrande.

Sai dai ba a samu matsala game da yadda aka shigo da Alessandro Diamanti ba, domin ya kasance fitaccen dan wasa a kungiyar wasan kwallon kafar kasar Italiya. Mai yiwuwa ne salonsa na taka leda da ya sha bamban da yanayin kulob din Evergrande ne ya sa ya kasa nuna bajimta sosai tun zuwan sa kulaf din.

A hannu guda yadda aka shigo da Alberto Gilardino kulaf din na Evergrande, gaskiya ana ganin ya saba wa ka'idojin kulob din ta fuskar dakko 'yan wasan ketare, domin dan wasan ba shi da kwarewa sosai, kana ba ya cikin irin 'yan wasan da Evergrande din take bukata, idan an yi la'akari da matsayinsa a filin wasa.

Kafin zuwan Marcello Lippi, shugaban kulob din Evergrande mista Liu Yongzhuo shi ke kula da aikin shigo da 'yan wasa daga ketare. Amma bayan zuwan Lippi sai ya karbi ragamar wannan aiki daga Liu, daga bisani kuma ya sanya dansa, wanda ke da wani kamfani mai kula da musayar 'yan wasa, ya kula da aikin shigo da 'yan wasa zuwa kulob din na Evergrande. Mai yiwuwa ne kuma domin neman riba ne daga wannan harka aka shigo da 'yan wasan 2 bisa farashi mai matukar tsada.

Sanin kowa ne dai cewa kulob din Evergrande yana da kudi sosai, wanda hakan ne ya sanya ya gayyatar Lippi a matsayin sa na fitaccen koci a duniya domin ya jagoranci kulob din. Amma duk da haka, shugabannin kulob din sun sa ido ga amfanin 'yan wasan ketare da ake shigowa da su. Musamman kuma ganin 'yan wasa 2 da Lippi ya gayyato ba sa taimakawa kulob din wajen cin kwallo, kana dansa ne neman kudi ta hanyar kula da wannan aikin, ya sa masu kulob din sake karbe ikon shigo da 'yan wasa daga hannun Lippi. Wannan batu watakila ya taimakawa niyyar Lippi ta barin Evergrande.

Ma iya cewa wannan batu ya dan raunana huldar dake tsakanin kulob din Evergrande da shi Lippi, amma a yawancin lokuta kulob din ya yarda da kwarewar Lippi, musamman ma a fannonin horar da 'yan wasa, da kula da tsarin kungiyar. Don haka, a bangarensa, kulob din na son ganin Lippi ya ci gaba da aiki a nan kasar Sin. Sai dai a nashi bangaren Lippi ya riga ya tsufa, kuma yana fatan komawa gida don zama tare da iyalinsa.

Tun dai lokacin da Lippi ya jagoranci kungiyar Evergrande ta lashe kofin gasar kwararrun kulflikan nahiyar Asiya, kocin wanda a lokacin yake da shekaru 67 a duniya, ya riga ya nuna niyyar sa ta koma gida. Kana kasancewar a shekarar kulob din Evergrande ya halarci gasanni da yawa, 'yan wasan kungiyar da shi kan sa Lippi sun yi matukar gajiya.

A baya dai Lippi ya ce kasar Sin babbar kasa ce, kana nahiyar Asiya tana da makeken fili, don haka shi da 'yan wasansa su kan kwashe awoyi 15 zuwa 16 domin halartar wasu wasannin da suka gudana cikin wannan yanki.

Lokacin da ya bar birnin Guangzhou inda Evergrande yake, Lippi ya ce ba zai jagoranci wani kulob din wasan kwallon kafa ba, kuma aikin da yake so shi ne zama kocin kungiyar kwallon kafa ta wata kasa. Duba da cewa kula da kungiyar kasa ba ya bukatar lokaci mai yawa, idan an kwatanta da na kungiyoyin kwallo daban daban.

Wani batun yana nuni ga yadda Lippi ke fatan komawa gida wurin iyalinsa maimakon aiki a ketare. An ce, yayin da yake aiki a nan kasar Sin, duk lokacin da aka yi hutu, ko da na tsawon makwanni 2 ne, ya kan hau jirgi ya koma Italiya, duk da matukar nisan kasar ta sa da kasar Sin.

Yanzu haka dai Lippi ya samu cimma burin sa na yin murabus daga mukamin mai horas da 'yan wasa a nan kasar Sin, amma taimakon da ya baiwa harkar kwallon kafa a kasar ta Sin bai kare a nan ba, ganin cewa ya bar ma'aikata masu tallafa masa suna ci gaba da aikinsu, gami da mataimakinsa na fannin horar da 'yan wasa Fabio Cannavaro, wanda ke nan kasar Sin a yanzu haka, mutanen da ake sa ran za su ci gaba da raya kulob din na Evergrande, har ya zama daya daga cikin fitattun kuloflika na duniya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China