in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Valdivia na nemi tsawaita wa'adin hutun sa domin ya sake murmurewa
2015-03-18 10:29:03 cri
Dan wasan kulaf din kwallon kafar Palmeiras Jorge Valdivia, ya mikawa hukumar gudanar da kwallon kafar kasar sa ta Chile, bukatar karin lokaci domin ya dada murmurewa kafin komawa taka leda, bayan raunin da ya samu a cinyar sa tun cikin watan Disambar bara. Idan dai har ya samu amincewar hakan, Valdivia ba zai buga wasannin sada zumunci da hukumar zata shirya tsakanin Chilen da Iran a ranar 26 ga watan nan na Maris, da kuma na Chile da Brazil a ranar 29 ga wata.

Da yake tsokaci game da hakan, kocin Palmeiras Oswaldo de Oliveira, ya ce Valdivia na fatan kulaf din sa zai sa-baki domin hukumar kwallon kafar Chilen ta amince da bukatar sa ta dada samun hutu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China