in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
PSV Ajax da Feyenoord sun dare saman teburin gasar Eredivisie
2015-03-18 10:27:26 cri
Kulaflikan PSV, da Ajax da Feyenoord sun dare matsayin koli a gasar Eredivisie ta kasar Netherlands, bayan wasannin karshen mako da suka buga.

PSV dai ta kwaci kanta da kyar a hannun FC Groningen a wasan ranar Lahadi, kafin daga karshe a tashi wasan 2 da 1. A dai wannan rana ita ma Ajax ta doke Heerenveen da ci 4 da 1. Kana alkalin wasan ya kori dan wasan Heerenveen Pele van Anholt, sakamakon keta da ya yiwa Anwar El Ghazi.

Yanzu haka dai PSV ce ta daya da maki 70, sai Ajax dake da maki 59 a matsayi na biyu, sai kuma Feyenoord ta uku da maki 51, yayin da AZ ke biye a matsayi na 4 da maki 47, bayan da ta rasa nasarar a wasan ta da Vitesse a ranar Juma'a, wasan da Vitesse ta lashe da ci 3 da daya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China