in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamus ta doke Georgia a wasan share fagen gasar zakarun Turai
2015-04-01 15:57:28 cri
Kulaf din kwallon kafar kasar Jamus ya doke takwaransa na Georgia da ci 2 da nema, a wasan share fagen gasar zakarun turai ta shekarar 2016.

Jamus dai ta samu nasarar wasan na ranar Lahadi ne ta kwallayen da 'yan wasan ta Marco Reus, da Thomas Mueller suka zura a raga tun cikin rabin lokaci na farko a wasan na rukunin D.

Poland wadda har yanzu ke kan gaba a rukunin ta samu nasara a dukkanin wasannin da ta buga, inda ta hada maki 11.

Scotland wadda ita ma ke cikin wannan rukuni ta doke Gibraltar 6 da 1. Matsayin da ya sanya Scotland din samun maki 10, daidai da na Jamus, yayin da Ireland ke biye da maki 8, take kuma fatan samun fita daga rukunin idan hali yayi.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China