Silva ya bayyana cewa, a cikin shekaru 20 da suka gabata, yawan mutanen da suke fama da matsalar yunwa ya ragu da miliyan 100 a kasar Sin. A cikin shirin raya kasa na M.D.D. da aka tsara a shekara ta 2000, an ce, an yi shirin rage rabin yawan mutanen da suke fama da talauci da yunwa zuwa shekarar 2015, kuma kasar Sin na kokarin cimma wannan buri. To, Amma, wannan ya danganta ne ga gyare-gyaren da gwamnatin Sin ke yi game da aikin gona da kauyuka da kuma saka musu jari.
A cikin bayanin, Mr. Silva ya ce, don kafa wata duniya da ta samu dauwamammen ci gaba da babu mayunwata, kamata ya yi kasashen duniya su cusa sabbin abubuwa wajen habbaka tattalin arziki, game da wannan, kuma kasar Sin tana da fasahohi masu amfani.(Bako)