Mr. Liu wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan a wajen bikin bude taron, ya kara da cewa Sin na burin yin hadin gwiwa da sauran kasashen Afirka, da kuma kafa sabbin dangantakar kasa da kasa bisa tushen hadin gwiwa da cimma moriyar juna.
Ya ce, gwamnatin kasar Sin na mai da hankali kwarai da gaske wajen gudanar da harkokin kasa bisa dokoki da kuma ciyar da tsarin dokokin kasa da kasa gaba, tana kuma fatan inganta wannan aiki a yayin gudanar taron na wannan karo.
A daya bangaren kuma, kasar Sin na mai da hankali sosai ga hadin gwiwa tare da kasashe masu tasowa wajen bunkasa harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, baya ga burinta na karfafa hadin gwiwa da kasashen Asiya da Afirka, karkashin wannan dandali na taron kungiyar tattaunawar harkokin doka na Asiya da Afirka. (Maryam)