An bukaci kasashen Afrika da su kara rubanya kokari domin kawar da yunwa da talauci ta hanyar kawo sauye sauye ga aikin noma, ganin cewa talauci na kasancewa wata babbar barazana ga ci gaban tattalin arzikin nahiyar, in ji wata jami'ar kungiyar tarayyar Afrika (AU) a ranar Talata. Rhoda Peace Tumusiime, kwamishinar AU a fannin tattalin arzikin karkara da noma, ta bayyana a cikin wata sanarwa a yayin taron ministocin kungiyar cewa, gwamnatocin kasashen Afrika sun dauki niyyar aiwatar da tsare tsaren ayyukan sake zuba jari a bangaren samar da abinci.
Shugabanni da gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar AU a shekarar 2014 sun nuna goyon baya kan wani tsari na gaba daya domin gaggauta sabbinta aikin noma ta hanyar kara zuba jari, amfani da fasahohin zamani da kawo sauye sauyen siyasa a wannan fanni. Niyyar siyasa game kawo sauyi kan aikin noma a nahiyar Afrika ta samu sakamako a bayyane. Kudaden da ake kebewa da manufofin siyasa a wannan bangare su ne a sahun gaba, in ji madam Tumusiime.
Kungiyar AU ta tabbatar da cewa, noma shi ne ginshikin ci gaban tattalin arziki da jama'a a nahiyar Afrika. Madam Tunusiime ta bayyana cewa, AU da abokan huldarta sun cimma ra'ayi guda kan wasu muhimman tsare tsare da za su taimaka wajen maido da martabar noma, da bunkasa tsarin samar da abinci a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara.
Haka kuma, kwamitin tarayyar Afrika da sabon tsarin ci gaban Afrika sun kaddamar a ranar Talata da wani sabon jadawalin aiki domin maido da martabar noma a Afrika, kawar da yunwa da rashin abinci mai gina jiki nan da shekarar 2025. (Maman Ada)