Kasar Najeriya na shirin kafa ayyukan yi miliyan 3,5 a bangaren aikin gona a shekarar 2015, don nuna cewa, ajandar kawo sauyi da ake bi a bangaren aikin gona zai samar da sakamako mafi alheri, in ji shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a ranar Laraba.
Ya zuwa yanzu, an kafa ayyukan yi miliyan uku a wannan bangare, in ji shugaban Najeriya tare da nuna cewa, noma zai iyar taimakawa kasar sosai wajen rage kaifin faduwar farashin danyen man fetur. Haka kuma ya nuna cewa, kasar ta taba samun da tan miliyan 21 na abinci a cikin shekaru uku na baya baya, abin da ya kafa wani yankin noma da rage kaifin faduwar darajar farashin abinci. (Maman Ada)