in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin aikin gona na taimakawa kasashen nahiyar
2015-03-13 10:16:16 cri

Kwararru a nahiyar Afirka sun yaba da yadda kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara suka amfana da kayayyakin noma na zamani da fasohohi sakamakon dangantakar Sin da Afirka a fannin aikin gona.

Emmanuel Tambi, darektan tsara manufofi da ilimantar da jama'a na dandalin binciken aikin gona a Afirka wanda ya bayyana hakan ya ce, sassan biyu sun amfana da wannan dangantaka matuka. Ya ce, baya ga binciken da Sin ta dauki nauyi kan aikin noma wanda hakan ya samar da guraben aikin yi ga matasan Afirka, hadin gwiwar ta kuma samar da kwarewar da ta taimaka wajen zamanantar da aikin noma a kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.

Tambi ya ce, nahiyar ta Afirka za ta bukaci nasarorin da Sin ta samu a fannin gona don cimma nata burin, saboda abincin da za a bukata sakamakon karuwar al'umma a nahiyar.

Wata sanarwa da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar ta nuna cewa, a shekaraun da suka gabata, kasar Sin ta hannun hukumar kula da abinci da aikin gona (FAO) ta tura kwararru 235 zuwa kasashen Mongolia, Najeriya, Uganda da wasu kasashe guda 6 don koya musu dabarun bunkasa aikin noma.

Wannan taimako da Sin ta samar ya samu yabo daga kasashen duniya, ciki har da asusun ba da lamuni na duniya IMF wanda ke cewa, hadin gwiwar Sin da Afirka ya taimaka wa ci gaban tattalin arzikin Afirka da sama da kashi 20 cikin 100. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China