in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya zama wajibi a kiyaye dangantakar abokantaka a tsakanin Rasha da Sin
2014-07-02 14:37:59 cri
Shugaban kasar Rasha Vlładimir Putin ya bayyana a ranar 1 ga wata cewa, abu ne da ya zama wajaba kasarsa ta kiyaye dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakaninta da kasar Sin.

Bisa labarin da fadar shugaban kasar Rasha ta bayar, an ce, Putin ya bayyana hakan ne a gun taron jakadun kasar Rasha dake kasashen waje. Yana mai da cewa, Rasha da Sin sun kasance abokai na kwarai a fadin duniya, kuma tushen hakan shi ne suna da ra'ayi iri daya kan manyan batutuwan duniya da na yankuna.

Kana Putin ya jaddada cewa, zumuncin dake tsakanin Rasha da Sin ba ya da nufin kawo barazana ga sauran kasashen duniya, kuma kasashen biyu ba za su kafa kawancen aikin soja ba. Ya ce, zumuncinsu ya kasance abin misali a fannin samun daidaito, girmama da juna da raya dangantakar kasashen biyu a karni na 21.

Putin dai ya gudanar da ziyara a kasar Sin tun daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Mayu, inda shugabannin kasashen biyu suka daddale hadaddiyar sanarwa kan raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakanin Sin da Rasha a sabon lokaci a birnin Shanghai dake kasar Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China