in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na kasar Sin na fatan ganin shirin "ziri daya da hanya daya" zai taimakawa shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya
2015-04-07 15:09:19 cri

Manzon musamman na kasar Sin kan batun yankin gabas ta tsakiya mista Gong Xiaosheng ya ziyarci Falasdinu a kwanakin baya, inda ya ce kamata ya yi a yi kokarin warware batun yankin gabas ta tsakiya daga dukkan fannoni. Ban da haka kuma, ya bayyana fatansa na ganin shirin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, na kafa zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa ta karni na 21, zai taimakawa raya tattalin arzikin yankin gabas ta tsakiya da shimfida zaman lafiya a yankin.

Mista Gong Xiaosheng, manzon musamman na kasar Sin kan batun yankin gabas ta tsakiya ya ziyarci Falasdinu a ranar 5 ga wata bisa agogon wurin, inda ya yi musayar ra'ayi tare da shugabannin Falasdinu, kan yanayin siyasar da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, da huldar dake tsakanin bangarorin 2, da dai makamantansu.

Falasidinu ta zama daya daga cikin kasashe masu goyon bayan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya a ranar 1 ga watan Afirilun da muke ciki. Dangane da batun, babban wakilin Falasidinu a fannin shawarwari mista Saeb Erekat, yayin da yake ganawa da manzon kasar Sin, ya ce, Falasdinu na fatan ganin kasar Sin za ta yi amfani da matsayinta na zaunanniyar mambar kwamitin sulhu na MDD, don magance zartas da wani kuduri a kwamitin sulhun da zai hana kotun hukunta manyan laifuka gudanar da aikinta yadda ya kamata. A cewar mista Erekat,

"Muna fatan kasar Sin za ta ba mu taimako, don daidaita matsalar da muke fuskanta ta hanyar sulhu, da magance nuna karfin tuwo. Muna girmama wa dokokin kasa da kasa, tare da fatan za a warware duk wata matsala a karkashin tsarin dokokin kasa da kasa. Saboda haka mun yi kokarin halartar tsare-tsaren dake karkashin dokokin kasa da kasa, ciki har da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya."

Haka zalika, manzon kasar Sin Gong Xiaosheng, ya gana da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, da ministan harkokin wajen Falasdinu Riad Malki, inda a bayan ganawartasu, mista Gong ya bayyana cewa, kasar Sin na fatan taka rawa a kokarin sa kaimi ga shawarwarin da ake yi tsakanin Falasidinu da Isra'ila, don kokarin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya. A cewar mista Gong,

"Yanzu ana fuskantar wani mawuyacin hali a kokarin da ake na kyautata yanayin siyasar yankin gabas ta tsakiya, domin ana samun bambancin ra'ayi sosai tsakanin bangarorin Falasdinu da Isra'ila, kuma suna nuna shakku da junansu. Muna fatan bisa kokarin da muke yi na sa kaimi ga gudanar da shawarwari, bangarorin 2 za su kara amincewa da juna, da tsayawa kan daidaita matsalar ta hanyar shawarwari."

Manzon musamman na kasar Sin ya kara da cewa, yayin da ake daidaita batun gabas ta tsakiya a nan gaba, ya kamata a yi kokarin warware matsalar daga dukkan fannoni, ta hanyar sa lura kan batun Falasdinu, maganar Syria, da dai sauransu. Har wa yau kuma, za a mai da hankali kan fannonin da suka hada da siyasa, tattalin arziki, al'adu, da dai makamantansu. Mista Gong ya ce,

"Dabarar da za a dauka don warware maganar gabas ta tsakiya a nan gaba, ba za ta kunshi yarjejeniyar sulhu da sauran takardun siyasa kawai ba, har ma za ta shafi yadda za a samar da tallafin jin kai, da sake gina kasa a bayan yaki, da farfado da tattalin arziki, da dai sauransu. Wato za a lura da fannonin siyasa, tattalin arziki, da al'adu, hakan zai sa a samar da wata dabarar da ta shafi dukkan fannoni, ta yadda za a samu damar tallafawa kokarin shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya."

Manzon kasar Sin ya kara da cewa, ta la'akari da niyyar warware maganar gabas ta tsakiya daga dukkan fannoni, shirin "ziri daya da hanya daya" da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar na da ma'ana sosai, ya ce,

"Shirin kafa 'ziri daya da hanya daya' zai iya zama wani muhimmin bangare na aikin shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya. Muna fatan ta hanyar gudanar da shirin, za a iya samar da gudunmowa ga kokarin wanzar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya, da samar da alheri da damammaki ga jama'ar yankin wadanda ke zama cikin wani yanayin yaki da rikici."

Haka zalika, mista Gong Xiaosheng ya bayyana fatansa na ganin karin kasashe sun sa kaimi ga gudanar da shawarwari tsakanin Falasdinu da Isra'ila, da kokarin kyautata yanayin da ake ciki, ta yadda za a aza tubali ga sake yin shawarwari tsakanin bangarorin 2.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China