in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyoyin kasa da kasa na sa kaimi wajen raya magunguna da fasahar jinya ta gargajiya ta kasar Sin
2015-03-16 16:39:10 cri

Kungiyar hadin gwiwa ta raya magunguna da fasahar jinya ta gargajiya ta kasar Sin ta kasa da kasa (WFCMS) da hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) sun kulla dangantaka a hukunce bayan kokarin da suka yi na tsawon shekaru goma. Shugabar kungiyar WFCMS She Jing ta bayyana a kwanan baya a nan birnin Beijing cewa, kulla dangantaka a hukunce tsakanin kungiyarta da WHO na da ma'ana sosai wajen daga matsayin magunguna da fasahar jinya ta gargajiya ta kasar Sin da sa kaimi ga bunkasuwar irin wadannan magunguna.

Kungiyar magunguna da fasahar jinya ta gargajiyar kasar Sin ce ta kafa wannan kungiyar ta WFCMS a shekarar 2003, wadda ta samun goyon baya daga kasashe da yankuna fiye da 100 a duniya, ta kasance wani dandalin kasa da kasa a fagen magunguna da ilmin likitoci. A cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, kungiyar WFCMS ta yi iyakacin kokari wajen raya magunguna da fasahar jinya ta gargajiyar kasar Sin a duniya tare da zurfafa hadin gwiwa tsakaninta da kungiyar WHO.

Shugabar kungiyar Madam She Jing ta nuna cewa, WHO ta shigo da kungiyar cikin mambobinta da ba na gwamnati ba, abin da ya alamanta cewa, WHO na mai da muhimmanci sosai kan kungiyarta, matakin da ya tabbatar da matsayin kungiyar a duniya da kuma sa kaimi wajen daga matsayin magungunan kasar Sin. Ta kara da cewa:

"WHO kungiya ce dake karkashin MDD, da ke ba da shawara da daidaita harkokin kiwon lafiya tsakanin gwamnatocin daban-daban, wadda kuma take kula da harkokin kiwon lafiya a duniya, tare da daukar nauyin ba da shawara ga harkokin kiwon lafiyar na kasa da kasa. Hadin gwiwa tsakanin WHO da kungiyarmu na da ma'ana sosai wajen sa kaimi ga bunkasuwar magunguna da ilmin likitoci na kasar Sin a kasashen daban-daban yadda ya kamata, da taka rawa wajen shigo da magunguna da ilmin likitoci na kasar Sin cikin tsarin kiwon lafiya na kasa da kasa."

An ba da labari cewa, magunguna da fasahar jinya ta gargajiya ta kasar Sin na da salo irin nata kuma an tabbatar da ingancinsu sosai, domin haka ne suke samun amincewa da karbuwa sosai a kasashen ketare. Ya zuwa yanzu, magunguna da fasahar jinya ta gargajiya ta kasar Sin sun yadu zuwa kasashe da yankuna 164, kuma an bude tasoshin ba da jiyya ta gargajiya ta kasar Sin dubu 100, masu ba da jiyya irin wannan kuma fiye da dubu 300 da hukumomin ba da ilmi irin wannan kimanin 700.

Wakilin WHO dake kasar Sin Bernhard Schwartlander ya nuna cewa, WHO ta amince sosai kan gudunmawar da fasahar jiyya ta gargajiya ta Sin ke bayar wajen tsarin kiwon lafiya na kasa, musamman ma na kananan sassa. Ya ce.

"Ana ta kara bukatar fasahar jiyya ta gargajiya sosai a halin yanzu. Ba ma kawai ta iyar warkar da cututuka musamman ma cututuka dake adabbar mutane ko da yaushe ba, hatta ma tana da amfani sosai wajen yin rigakafi da kiwon lafiya. Saboda haka, ya kamata mu karfafa inganci da karfin fasahar jiyya ta gargajiya, ta haka ne za a karfafawa mutane kwarin gwiwa kan irin wannan fasaha, ta yadda za su kara amincewa da fasahar gargajiya da daga matsayinta cikin tsarin kiwon lafiya gaba daya nan gaba."

Amma, a sa'i guda Mr Schwartlander ya ce, kalubale mafi tsanani da magunguna da fasahar jiyya ta gargajiya ta kasar Sin ke fuskanta wajen shiga kasuwar kasa da kasa shi ne ma'aunin magunguna da masu aikin jiyya dake amfani da fasahar irin wannan. Ya ce,

"Yanzu, magunguna da fasahar jiyya ta gargajiyar kasar Sin ta shiga kasuwar kasa da kasa, kasashen da dama na iyar samu irin wadannan magunguna da fasahohi. Duk da haka kuma, muna da karancin wani ma'aunin da ya dace, mutane da yawa na shakku sosai kan likitoci masu amfani da fasahar jiyya ta gargajiyar kasar Sin. Sabo da haka, akwai matukar bukata wajen kafa ma'aunin magungunan da na masu aikin jiyya dake amfani da fasahar jiyya ta gargajiya ta kasar Sin, hakan zai iya daga matsayi da ingancinta, ta yadda jama'ar kasa da kasa za su kara amince da ita."

An ba da labari cewa, WFCMS za ta gabatar wa WHO ma'auninta na Sinanci da Turanci, tare da baiwa WHO taimakon kimiyya bisa takardunta, da ba da rahotani kan nazarin da kungiyar ta yi a fannin ma'aunin kasa da kasa, har ma da samar da shaidun tabbatar da amfani da ingancin magunguna da fasahar jiyya ta gargajiya ta kasar Sin, ta yadda za a iya kara raya su a kasashen ketare. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China