in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi alkawarin taimakawa kokarin dakile cutar Ebola har aka kau da ita gaba daya
2015-03-24 16:01:20 cri

Mataimakiyar darektar kwamitin lafiya da takaita haihuwa na kasar Sin, madam Cui Li, ta ce gwamnatin kasar Sin ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa, da su ci gaba da daukar takamaiman matakai na tallafawa kasashen dake yammacin Afirka a kokarin kau da cutar Ebola.

Duk da cewa an samu nasarar hana yaduwar cutar Ebola a farkon wannan shekara ta bana, amma samun karin wasu mutanen da suka kamu da cutar a kwanakin baya a kasar Laberiya, ya tilastawa kasashen duniya sake yin hattara wajen magance kamuwa da cutar.

Bisa alkaluman da hukumar lafiya ta duniya WHO ta gabatar, an ce har ya zuwa ranar 11 ga watan Maris din nan, cutar ta riga ta shafi mutane dubu 24 a kasashen Guinea, da Laberiya da Saliyo, wadanda cikinsu kimanin dubu 10 suka mutu. Annobar da ta fi yaduwa a yammacin Afirka a wannan karo ta wuce sauran cututtukan da suka taba abkuwa a tarihi, a bangaren yawan kasashe da ta tsallaka, da tsanantar ta, gami da wahalar dakile ta.

A yayin da ake kokarin dakile wannan cuta, kasashe daban daban sun samar da tallafi ga yammacin Afirka, cikinsu har da kasar Sin. A wannan karo, an kira wani taron kara-wa-juna-ilimi na kasa da kasa dangane da kwayoyin cutar Ebola a nan birnin Beijing, inda a ranar Litinin 23 ga wata, kwararru da masana fiye da 150, wadanda suka zo daga hukumar WHO, da cibiyar rigakafi da shawo kan cututtuka ta kasar Sin, gami da sauran wasu kungiyoyin na kasar Sin da na wajen kasar, suke tattaunawa game da yanayin da ake ciki wajen dakile cutar Ebola a yammacin Afirka.

A wajen bikin budewar taron, an nuna wani bidiyon taya murna na mataimakin darektan hukumar WHO Bruce Aylward, wanda ya ambaci gudummowar da gwamnatin kasar Sin ta samar a kokarin dakile cutar Ebola, ciki hadda samar da kayayyaki na dalar Amurka miliyan 120, da tura tawagar tallafi ta mutane fiye da 800, wadanda suka yi jinyar masu kamuwa da cutar fiye da 9000. A cewar Aylward,

"Kasar Sin ta tura wasu kwararru fiye da 50 don horar da ma'aikata masu kula da lafiyar jama'a a Afirka, gami da taimakawa wajen kafa wasu dakunan gwajin halittu a yammacin Afirka. Wadannan dakunan gwaji za su ba da taimako ga jama'ar kasashen yammacin Afirka, don su gano masu dauke da cutar ta Ebola, da kuma nazari kan wannan cutar. A shekarar 2014, mun samu wasu alkaluman da suka shafi cutar Ebola, da cibiyar shawo kan cututtuka ta kasar Sin ta aiko mana, lamarin da ya sanya mu farin ciki sosai. Kasar Sin ta samar da gudummowa sosai a kokairn dakile wannan cutar."

Ban da samar da kayayyaki, da tura kwararrun likitoci, kasar Sin ta aike da wasu kwararru zuwa kasashen dake fama da cutar Ebola, inda suke kula da aikin wayar da kan jama'ar wurin, game da ilimin fannin kiwon lafiyar jama'a, wanda hakan tamkar kafa wata tawagar likitoci ce, da ba za ta bar kasar da cutar Ebola ta shafa ba.

A cewar babban darektan cibiyar rigakafi da shawo kan cututtuka ta kasar Sin, mista Wang Yu,

"Wani babban batu da ya haddasa yaduwar cutar Ebola shi ne rashin tsaro a fannin jana'izar mutanen da suka rasu sakamakon cutar, da yadda a kan gaza sanar da samun karin mutanen da suka kamu da cutar cikin lokaci. Ta la'akari da haka, tilas ne a wayar da kan jama'a a wannan fanni, gami da canza salon jana'iza, don dakatar da yaduwar cutar Ebola. Zuwa watan Maris na shekarar 2015, kasar Sin ta tura kwararrun masu aikin likitanci don horar da mutane kimanin dubu 13, na kasashe 9 dake yammacin Afirka, wadanda suka kunshi jami'an lafiya, da 'yan sanda, da malamai, da jami'an gwamnati, da dai sauransu. "

Zuwa yanzu, mutane masu dauke da kwayoyin cutar Ebola a duniya kalilan ne, haka kuma ana kan hanyar kau da cutar baki daya. Sai dai, a ganin Cui Li, mataimakiyar darektar kwamitin lafiya da takaita haihuwa na kasar Sin, ya kamata a kara nuna hattara dangane da yadda ake ci gaba da samun mutanen da suke kamuwa da cutar. Saboda haka, madam Cui ta yi kira, a madadin hukumar kasar Sin, ga kasashe daban daban, cewa ana fatan ganin gamayyar kasa da kasa za su kara daukar wasu matakai na tallafawa kasashen dake yammacin Afirka, a kokarin kau da cutar Ebola gaba daya. Cui Li ta ce,

"Tallafin da kasar Sin take samarwa a fannin kiwon lafiya zai kunshi bangarori 3. Na farko, za a taimakawa kasashen Afirka a kokarinsu na kyautata tsarin aikin likitanci da kiwon lafiya. Na biyu, za a kara horar da ma'aikatan kasashen Afirka masu aikin likitanci. Sa'an nan na uku za a taimakawa kokarin kafa wata cibiyar shawo kan cututtuka a karkashin inuwar kungiyar kasashen Afirka AU, don daukaka matsayin nahiyar Afirka a fannin kula da lafiyar jama'a."(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China