in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron tattaunawa kan hadin gwiwar kiwon lafiya a tsakanin Sin da kasashen Afirka
2015-03-27 16:44:01 cri

An kaddamar da taron tattaunawa game da hadin gwiwar kiwon lafiya tsakanin Sin da kasashen Afirka karo na 5, taron da aka yiwa lakabi da "sa kaimi ga tabbatar da lafiyar daukacin jama'a, da fadada safarar magunguna".

An dai bude taron ne a jiya Alhamis a nan birnin Beijing, inda wakilai masu halartar taron suka yi kira ga Sin, da kasashen Afirka su kara inganta dangantakar hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya daga dukkanin fannoni.

Wakilai a fannin kiwon lafiya, da ma'aikatan hukumomin ba da gudummawa, da na kamfanoni da gwamnatoci daga Sin da kasashen Afirka, da sauran kasashen duniya fiye da 350 ne suka halarci taron tattaunawar da aka gudanar a nan birnin Beijing, inda aka tattauna kan abubuwa da dama, ciki hadda kalubalen da ake fuskanta game da hadin gwiwar kiwon lafiya a tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Shugaban sashen hadin gwiwar kasa da kasa na kwamitin kiwon lafiya, da kayyade iyali na kasar Sin Ren Minghui, ya bayyana a gun taron cewa, tun lokacin da Sin ta fara tura rukunin likitoci a karon farko zuwa nahiyar Afirka a shekarar 1963, ya zuwa yanzu an ci gaba da tura likitoci da yawan su ya zarta dubu 20, zuwa kasashe da yankuna 45 dake nahiyar. Ya ce wadannan jami'an lafiya sun ba da taimakon jinya ga al'ummar Afirka kimanin miliyan 230.

Kaza lika tun daga shekarar 2014, Sin na bada gudummawar kiwon lafiya mafi girma ga kasashen Afirka a fannin yaki da cutar Ebola. Ren Minghui ya bayyana cewa,"Tun bullar cutar Ebola a yammacin Afirka a watan Maris na shekarar 2014, gwamnatin kasar Sin ta samar da gudummawa har zagaye hudu, wadda kimar ta ta kai kudin Sin RMB miliyan 750, ta kuma tura likitoci kimanin dubu daya zuwa kasashen Guinea, da Saliyo, Liberia da kasashen dake dab da kasashen uku. Ta kuma karbi tare da bada jinya ga wadanda suka kamu da cutar fiye da dari 8, ta kuma ba da horo a fannin kiwon lafiya ga mutane fiye da dubu 12, tare da tura masana zuwa aiki karkashin tawagar manzon musamman ta MDD, da ta hukumar kiwon lafiya ta duniya don yaki da cutar Ebola."

Ren Minghui ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tura likitoci zuwa kasashen Afirka don taimakawa aikin yaki da cutar Ebola, kana Sin tana fatan taimakawa kasashen Afirka wajen inganta aikin sa ido, da bincike kan cututtukan dake addabar kasashen Afirka, don bada gudummawa ga kiwon lafiyar dukkan duniya.

Da yake tsokaci game da wannan batu, mamba mai kula da harkokin zamantakewar al'umma na kwamitin kungiyar AU Mustapha Sidiki Kaloko, ya yi nuni da cewa hadin gwiwar kiwon lafiya a tsakanin Afirka da Sin na da dadaden tarihi, kuma Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen nuna goyon baya ga nahiyar Afirka a fannin kiwon lafiya. Kaloko ya bayyana cewa,"Sin ta taka muhimmiyar rawa a aikin 'yantar da kasashen Afirka, kana ta dauki matakai, da cika alkawarinta na taimaka musu wajen cimma burin bunkasuwa. Kungiyar AU ta nuna farin ciki ga hadin gwiwar dake tsakaninta da Sin. Nan gaba ya kamata a sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa tsakaninsu a fannoni daban daban, don ba da tabbaci na cimma burin inganta kiwon lafiyar dukkan jama'ar kasashen Afirka."

Shugaban rukunin kula da tsarin kiwon lafiya da ba da hidima na sashen Afirka, a hukumar kiwon lafiya ta duniya Delanyo Dovlo ya bayyana cewa,"Muna fatan za a kafa dangantakar hadin gwiwa ta cimma moriyar juna a tsakanin Sin da Afirka, musamman wajen kyautata karfin likitoci, da kafa tsarin sa kaimi ga more fasahohi da ilmi, da kafa hukumomin kasa da kasa da yankuna, wanda zai kula da harkokin rarraba magunguna, da sauran hidimomin kiwon lafiya.

Taron tattaunawa kan hadin gwiwar kiwon lafiya a tsakanin Sin da Afirka, wata dama ce ta kara yin mu'amala, da kafa tsarin hadin gwiwar cimma moriyar juna. Ina fatan za mu sa kaimi wajen yin kokari tare, don kirkiro kyakkyawar makoma ta hanyar wannan taro." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China