in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin dake Namibia ya jinjinawa dangantakar kasashen biyu
2015-03-26 17:02:57 cri

Shekarar bana ita ce cikon shekaru 25 da kafa dangantakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da kasar Namibia, game da hakan ofishin jakadancin kasar Sin dake Namibia ya shirya nune-nunen wasu hotunan tarihi, domin maimaita yadda aka yi kokarin kyautata huldar dake tsakanin kasashen biyu cikin tsawon wadannan shekaru 25.

Game da hakan jakadan Sin dake kasar Namibia Xin Shunkang ya bayyana cewa, a halin yanzu kasar Sin da kasar Namibia na kasancewa abokan arzikin juna bisa fannoni daban daban, kana kasar Namibia tana daya daga cikin kasashen da kasar Sin ta fi zuba jari ciki, haka kuma ana ci gaba da zurfafa dangantakar kasashen biyu yadda ya kamata.

Saminu Alhassan na dauke da cikakken rahoton game da hakan:

Shekarar bana ita ce shekara cikon ta 25, tun bayan da kasar Namibia ta samu 'yancin kai, kana cikon shekaru 25 da aka kafa huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Namibia. Cikin wadannan shekaru kasar Sin ta samar wa kasar babban taimako da goyon baya, a yayin da Namibia ke neman 'yancin kai daga kasar Afirka ta Kudu, matakin da ya kafa zumunci mai zurfi tsakanin shugaban farkon kasar Namibia Samuel Daniel Nujoma, da shugabannin kasar Sin, kamar su Mao Zedong, da kuma Zhou Enlai. Kaza lika a ganin jakadan kasar Sin dake kasar Namibia Xin Shunkang, ana ci gaba da zurfafa dangantakar zumunci dake tsakanin kasashen biyu bisa fannoni daban daban, tun bayan kulla huldar diflomasiyya a tsakanin Sin da Namibia, ya ce,

"Na farko shi ne, kasashen biyu na ci gaba da karfafa dangantakarsu a fannin siyasa, kuma wannan shi ne ci gaba na zumuncin gargajiyar kasashen biyu, inda dangantakar kasashen biyu ta kai ga kasancewa abin koyi tsakanin dangantakar kasar Sin da ragowar kasashen Afirka.

Sa'an nan kuma, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu na ci gaba da bunkasa, duk kuwa da kasancewar Namibia karamar kasa, amma ta na da albarkatun ma'adinai, da ruwa, kana tana da albarkatun kiwon dabbobi mai inganci, al'amuran da ke matukar biyan bukatun kasuwannin kasar Sin. A daya hannun kuma, kasar Sin tana taimakawa kasar Namibia wajen cimma burinta na raya masana'antu, da samar da guraben aikin yi, da kuma kyautata zaman rayuwar al'ummominta."

A halin yanzu, manyan kamfanonin kasar Sin na zuba jari a kasar Namibia a fannin ma'adinai. A shekarar 2012, babban kamfanin raya sha'anin nukiliya ta CGNPC na kasar Sin, da asusun Sin da Afirka, sun sayi shirin hakar ma'adinin na Uranium a wani yankin kasar ta Namibia, inda suka kafa wani kamfanin hadin gwiwa da kamfanin ma'adinan kasar ta Namibia, da wasu hukumomin da abin ya shafa a kasar, domin gudanar da harkokin shirin sarrafa ma'adinin Uranium na kasar ta Namibia, harkar da aka sanya kudi har dalar Amurka biliyan 5 cikin ta.

Dangane da hakan, Jakada Xin na kasar Sin ya bayyana cewa,

"Wannan ya kasance abin koyi a fannin hadin gwiwar Sin da Namibia, watau kafa wani kamfanin dake gudanar da ayyukansa bisa fasahohin zamani na kasa da kasa, wanda kuma ya sami goyon baya daga gwamnatocin kasashen da abin ya shafa. Wannan kamfanin da aka kafa wajen raya sha'anin sarrfa Uranium, zai haifar da babban tasiri ga farashin ma'adinin Uranium, kuma zai daukaka matsayin kudin kayayyakin da ake samarwa a gida GDP na kasar Namibia, da kuma samar da karin guraben aikin yi ga jama'ar kasar, ta yadda harkokin dake shafar ba da ilmi, da kiwon lafiya, da kuma ginin birane da dai sauransu a kasar, dukkansu za su sami kyautatuwa."

Kaza lika, a ganin Mr. Xin, banda sha'anin ma'adinai, akwai fannoni da dama masu kyau da kamfanonin kasar Sin za su iya zuba jari a ciki, ciki har da ayyukan samar da ruwa, da inganta noma, da samar da kayayyakin more rayuwa da dai sauransu. Kana gwamnatin kasar Namibia na maraba da kamfanonin ketare wajen zuba jari a yankunan ta, saboda haka ne ma ta fitar da manufofi da dama dangane da wannan harka, ya ce,

"Kasar Namibia na gudanar da budaddun manufofin zuba jari, kana tana da albarkatu da dama, idan akwai fasahohi da kuma kudade, za mu iya zama tare domin tattaunawa game da yin hadin gwiwa, wanda hakan ke janyo hankulan kamfanonin kasar Sin da dama."

Bayan samun 'yancin kanta shekaru 25 da suka gabata, Namibia ta samu babban ci gaba a fannoni daban daban, da suka hada da yanayin zuba jari, da sufuri, da kuma dangantakar dake tsakaninta da kasashen ketare. Kana bunkasuwar tattalin arzikinta ya kasance a matsayi na gaba tsakanin kasashen kudancin nahiyar Afirka. A ganin Mr. Xin, nasarorin da kasar ta samu na da alaka da samun wata jam'iyyar dake mulki mai karfi, da manufofin gwamnati masu nagarta, da kuma yadda ake bude kofa ga kasashen waje.

Mr. Xin ya kuma nuna fatansa cewa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Namibia za ta ci gaba da karfafa, domin cimma moriyar juna, da kuma tallafawa jama'ar kasashen biyu yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China