in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta cafke mutane 5 da take zarginsu da hannu kan harin jami'ar Garissa
2015-04-04 20:43:18 cri
Kasar Kenya ta cafke wasu mutane uku a ranar Jumma'a bisa binciken da ake game da harin jami'ar Garissa dake arewa maso gabashin kasar Kenya, adadin da ya kai zuwa mutane biyar da ake zargi tare da tsare su, in ji ministan cikin gidan Kenya Joseph Nkaissery a ranar Asabar. Mutanen uku da ake zargi, zai yiwu cewa suna da hannu tare da wanda ya shirya kai harin ta'addanicin na Garissa, Muhamed Gamadhere, kuma an cafke su ne a kan iyakar Somaliya a yayin da suke kokarin tserewa daga kasar Kenya a ranar Jumma'a.

A cikin wata sanarwa a ranar Asabar, kungiyar masu kaifin kishin islama Al-Shebab dake da alaka da kungiyar Al Qaida ta yi barazanar cigaba da kai sabbin hare hare kan kasar Kenya, bayan wanda ta kai a jami'ar Garissa da ya halaka mutane 148 tare da jikkata wasu da dama. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China