in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu babban ci gaba wajen warware matsalar nukiliyar Iran
2015-04-03 17:06:54 cri

An kawo karshen shawarwarin ministocin harkokin waje kasashe shida da batun da nukiliyar Iran ya shafa, wadanda suka hada da Amurka, Sin, Ingila, Burtaniya, Rasha da Faransa da ita kanta kasar Iran a jiya ranar Alhamis a birnin Lausanne na kasar Switzerland. A matsayin wani hakikanin sakamako da aka samu a yayin wadannan shawarwarin, bangarori daban daban sun samar da wata hadaddiyar sanarwa, inda suka cimma ra'ayi daya game da warware wasu muhimman matsalolin da suka kawo cikas wajen warware batun nukiliyar Iran. Wannan ya nuna cewa, an cimma wani muhimmin mataki wajen warware wannan batu a siyasance daga dukkan fannoni, bayan an shafe shekaru kusan 12 ana kokarin cimma mafita kan wannan batu.

A yammacin wannan rana a babban dakin taro na jami'ar koyon kimiyya da fasaha ta Lausanne ta kasar Switzerland, bayan shawarwarin da aka yi cikin mawuyacin hali na kwanaki 15, bangarori daban daban na jiran wani muhimmin lokaci.

"Yau, mun taka wani muhimmin mataki, inda muka cimma wani shiri na warware muhimman batutuwa game da yarjejeniyar karshe. An samu wannan sakamako ne ta hanyar hadin kai da kokarin da bangarori daban daban suka yi, shi ne kuma ya nuna kudurin siyasa da bangarorin suka tsaida da kuma fatan alheri nasu."

A daren wannan rana da karfe 7 da minti 40, babbar wakiliyar kungiyar EU mai kula da harkokin diplomasiyya da manufofin tsaro madam Federica Mogherini, da ministan harkokin wajen kasar Iran Javad Zarifi sun bayar da wannan sanarwa tare. Kamar yadda aka saba yi, da farko a madadin kasashe 6 da batun nukiliyar Iran ya shafa, madam Mogherini ta karanta sanarwar da Turanci. Daga baya kuma, ministan harkokin wajen kasar Iran Zarif ya kara karanta sanarwar da harshen Farsi.

Ko da yake wannan hadaddiyar sanarwa da aka cimma ta samu latti na kwanaki biyu bisa lokacin da aka tsaida, da sauyi kadan kan sunan takardar, amma abubuwan dake cikin sun hada da muhimman fannonin da suka shafi warware matsalar nukiliyar Iran, hakan ya nuna cewa, bangarorin daban daban sun cimma muhimmin ra'ayi daya kansu. Abin da ya fi muhimmanci daga cikinsu shi ne, hana shirin nukiliyar Iran don tabbatar da cewa, za ta yi amfani da makamashin nukiliya domin makasudin zaman lafiya, a waje guda kuma akwai bukatar kasashen duniya su kawar da takunkumin da suka kakabawa Iran.

Game da batun tace sinadaran Uranium, sanarwar ta amince da kasar Iran da ta ci gaba da shirinta na amfani da makamashin nukiliya cikin lumana, sa'i daya sanarwar ta kayyade matsayi kan karfin tace sinadaran uranium na kasar Iran, da yawan irin sinadaran da take tanada. Kana an amince da Iran da ta kiyaye na'urorin nukiliyarta a Natanz, amma dole ne za ta yi gyare-gyare kan na'urorin nukiliya na Fordo, da babbar na'ura mai inganta ruwa ta Accra a karkashin taimakon kasashen duniya. Bayan haka kuma, sanarwar ta amince da Iran da ta yi nazari kan sabuwar na'urar sarrafa uranium, amma dole ne ta gudanar da aikin bisa shirin da aka tsaida.

A nasu bangaren ma, bayan da hukumar makamashin nukiliya ta duniya ta yi bincike da kuma tabbatar da cewa, kasar Iran ta cika alkawarin da ta dauka, to kungiyar EU da kasar Amurka za su kawar da takunkumin da suka sanya wa kasar Iran a fannonin tattalin arziki da kudi. Kwamitin sulhu na MDD ma zai zartas da wani sabon kudiri, inda za a dakatar da kudurin da ya zartas game da takunkumi kan Iran bayan an daddale yarjejeniyar batun nukiliyar Iran a dukkan fannoni, kana kuma za a cimma wata yarjejeniya kan wasu matakan da aka kayyade cikin wani lokacin da za a tsara.

Haka zalika sanarwar ta bayyana cewa, wannan shirin da aka cimma ya samar da harsashi mai muhimmanci ga shawarwarin, da kuma daddale wata yarjejeniya kan batun nukiliyar Iran daga dukkan fannoni.

"A cikin 'yan makwani masu zuwa ko 'yan watanni masu zuwa, za mu shirya wata takarda game da yarjejeniyar daga dukkan fannoni, za mu yi kokarin kammala wannan aiki kafin ranar 30 ga watan Yuni." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China