Bisa labarin da wakilinmu ya samu daga kwalejin kula da harkokin kimiyya da likitanci na sojinna kasar Sin, an ce, bayan da Anna Kross, wata sojar Birtaniya mai shekaru 25 da ta kamu da cutar Ebola, ta sha wani sabon maganin MIL 77 da kwalejin din da masana'antu masu harhada magunguna guda biyu suka kirkiro tare domin kashe kwayoyin cutar, ta samu warkewa a wani asibitin dake birnin London a Biraniya. Haka kuma, bayan da sauran 'yan Birtaniya 2 da ake zaton kamuwa da cutar Ebola sun sha maganin a matakin yin rigakafi, sun fara farfadowa, wadanda yanzu suke cikin koshin lafiya. Yanzu, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, Canada, Birtaniya da kungiyar likitoci ta kasashen duniya sun gabatar da bukatunsu na neman wannan maganin.
Bisa sakamakon bincike da hukumar kiwon lafiya ta kasar Canada ta yi, an ce, maganin MIL 77 da kasar Sin ta kirkiro, yana da amfani da inganci, wandaba ya kawo illa sosai ga lafiyar jiki, kuma idan aka kwatanta shi da maganin da kasar Amurka ta samar, na kasar Sin ya fi kyau gare shi.(Bako)