Tsohuwar 'yar wasan gudun kankara daga kasar Amurka Michelle Kwan, ta yi jawabi yayin taron, ta na mai cewa lokacin da mata ke shiga wasannin motsa jiki, da harkokin zamantakewar al'umma, da bada ilmi a makarantu, da kuma takara a ayyukansu, za su iya kara taimakawa wajen kirkiro hanyoyin inganta zamantakewar al'umma mai karfi, da zaman karko.
Kana Kwan ta bayyana cewa, kara samar da iko ga mata ta hanyar shiga wasannin motsa jiki, bai tsaya ga samar musu da na'urorin wasanni kawai ba, har ma da samar musu da damar cimma burinsu yadda ya kamata.
Shekarar bana dai shekara ce ta cika shekaru 20 da gudanar da babban taron mata na duniya, kuma MDD za ta gudanar da wasu ayyuka na kira ga samar da adalci ga mata, da baiwa mata iko da damar samun bunkasuwa.(Zainab)