in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa dokar hana zirga-zirga a jihar Rivers dake kudancin Najeriya
2015-03-31 19:54:19 cri
Mahukuntan jihar Rivers dake kudancin Najeriya, sun bayyana kafa dokar hana zirga-zirgar jama'a, tun daga karfe 7 na yamma zuwa karfe na safiyar ko wace rana, biyowa bayan wata zanga-zangar siyasa da wasu gungun matan jihar suka gudanar a jiya Litinin.

Cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai a birnin Fatakwal fadar mulkin jihar ta Rivers, sakataren gwamnatin jihar George Feyii ya bukaci daukacin al'ummar jihar da su kiyaye wannan doka, yana mai cewa an kafa ta ne domin tabbatar da doka da oda, tare da kaucewa barkewar rikici.

A jiya Litinin ne dai dandazon mata magoya bayan jam'iyyar adawar APC suka yi jerin gwano sanye da bakaken kaya, suka kuma dunguma ofishin hukumar zaben kasar INEC reshen jihar, domin mika korafi game da abun da suka kira magudin zaben da aka tafka a jihar, sai dai kafin isar su ofishin na INEC ne 'yan sanda suka harba musu barkonon tsohuwa, nan take kuma suka tarwatse tawagar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China