in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeriya ta bude kan iyakokinta na kasa
2015-03-30 10:33:32 cri

Gwamnatin tarayyar Nigeriya ta umurci hukumar shige da ficen kasar da ta bude kan iyakokinta na kasa daga karfen 12 ranar Lahadi, kamar yadda wani babban jami'in hukumar ya tabbatar.

David Parradang, babban komtrolan hukumar ya ce, an bayar da wannan umurni a daren ranar Asabar ganin cewar, kasar tana bukatar dawo da hada hadarta a ciki da wajen kan iyakokin da aka rufe tun ranar Laraba.

Mr. Parradang ya ce, duk da cewa hukumar zaben kasar ta kara lokacin zaben har zuwa ranar Lahadi, gwamnati ta ba da wannan umurni da la'akarin cewa, zabe a wadannan wurare dake da kan iyakoki zai yiwu a kammala zuwa karfen 12 rana.

Ya ce, bude kan iyakokin kasar ta kasa ba zai shafi zaben ba, ta ko wane hanya ganin yadda jami'an hukumar ke sintiri ba dare ba rana a wuraren. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China