Jam'iyya mai mulki a Nigeriya ta bayyana cikas din da na'urar katin zabe ta kawo na kasa shigar da sunan shugaban kasar Goodluck Jonathan a ranar Asabar a matsayin abin kunya ga kasa baki daya.
Kakakin jam'iyyar ta PDP Olisa Metuh a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadin ya ce, jihohi da dama sun gamu da irin wannan cikas din, a don haka ya bukaci hukumar zaben mai zaman kanta da ta ba da bayani mai gamsarwa.
Mr. Metuh ya ce, rashin iya karanta sunayen masu jefa kuri'a da katin ya yi a zaben ranar Asabar na shugaban kasar da na 'yan majalissun tarayya a duk fadin kasar abu ne da za'a iya kauce mashi, a ganin shi, hakan da ya yuwu idan har hukumar zaben ta saurari shawarwarin da 'yan Nigeriya, kungiyoyi da ma ita kanta jam'iyyar ta PDP suka yi ta bayarwa game da kai wadannan na'urorin zabe ba tare da an gwada su ba. (Fatimah)