in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeriya na tattara sakamakon karshe na babban zaben kasar
2015-03-31 09:41:48 cri

Nigeriya ta fara tattara sakamakon karshe na zaben da aka yi a karshen makon da ya gabata, inda shugaban hukumar zaben ta kasar Farfesa Attahiru Jega yake jagoranta cikin tsatsauran matakan tsaro.

Shugaban hukumar zaben ya kaddamar da fara tattara sakamakon, tare da gabatar da kwamishinonin zaben jihohin da suke wajen a wannan lokacin a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

Jami'an tsaro sun kafa shingayen a hanyoyi da dama wadanda su ma suke lura da tantance manema labarai da jami'an zaben dake wajen bayan da aka kara kwana daya a zaben da aka fara ranar Asabar zuwa Lahadi, sakamakon yawan korafin rashin isan kayayyakin zabe, musamman ma na'urar dankwala zaben da a wassu wuraren ba ta yi aiki ba.

Wannan zaben dai, an yi shi cikin kwanciyar hankali, amma ana zaman game da yadda zullumin sakamakon zaben ke tafiyar hawainiya. Zaben da masana ke ganin shi ne wanda aka fafata kwarai a tarihin kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afrika.

Shugaban kasar mai ci yanzu Goodluck Jonathan yana fuskantar babban kalubale daga 'dan takarar jam'iyyar adawa ta APC, kuma tsohon shugaban kasar a mulkin soja Muhammadu Buhari. Mutane da dama na fatan sabon shugaban zai kawo sauki ga tabarbarewar tattalin arziki da faduwar darajar mai ta kawo, da kuma barazanar tsaro da kasar ke fuskanta daga mayakan Boko Haram. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China