Ministan ma'aikatar harkokin cikin gidan Najeriya Abba Moro, ya ce, an sake bude tashoshin jiragen ruwan kasar, bayan da aka rufe su a ranar Laraba 25 ga wata.
Moro ya ce, a baya an rufe tashoshin ne domin tabbatar da tsaro, gabanin gudanar babban zaben kasar, sai dai daga bisani an canza wannan shawara don ba da damar ci gaba da gudanar da harkokin raya tattalin arziki kamar yadda aka saba.
Ministan ya kara da cewa, daukacin sassan jami'an tsaron dake kula da tashoshin ruwan za su kasance cikin shiri, domin tabbatar da gudanar zaben Najeriyar cikin kyakkyawan yanayi. (Saminu)