Karamin ministan ma'aikatar tsaron Najeriya Austin Akobundu, ya ce, babu bukatar nuna fargaba, game da matakin tura sojoji runfunan zabe, domin a cewar sa za su taimakawa sauran jami'an tsaro ne kawai, wajen tabbatar da doka da oda.
Mr. Akobundu, wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a jiya Alhamis, ya kuma bukaci al'ummar Najeriya da su kwantar da hankulansu, domin kuwa sojojin ba za su tsoma hannu cikin harkokin zabe ba.
Ya ce, alhakin dakarun sojin kasar ne su tabbatar da bin doka da oda a duk lokacin da aka bukaci hakan, baya ga aikin kare kasa da suke aiwatarwa.
Za dai a kada kuri'u a zaben shugaban kasa, da na 'yan majalisar tarayyar Najeriya ne a gobe Asabar 28 ga watan nan na Maris. (Saminu)