in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin tana son samar da karin damar neman bunkasuwa ga duk duniya
2015-03-29 18:21:48 cri

A ran 29 ga wata, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da mambobin kwamitin dandalin tattaunawa na Asiya na Boao a garin Boao dake lardin Hainan na kasar.

Mr. Xi ya nuna cewa, a cikin shekaru 10 ko fiye da suka gabata, dandanlin tattaunawa na Asiya na Boao ya samu ci gaba a kai a kai. Sannan ya jaddada cewa, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen Asiya, har ma duk duniya tana kuma samun sauye-sauye, makomarsu ma tana kusantar da juna kwarai. Kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan matsayin neman ci gaba cikin lumana, tana kuma kokarin kafa sabuwar huldar tsakanin kasa da kasa bisa ka'idar moriyar juna da neman samun nasara tare. Bugu da kari, tana bin ka'idar hada kan sauran kasashen duniya, amma ba kafa ta kamar wata kungiya ba, ta yadda za ta iya kafa wani tsarin abokantaka dake shafar duk duniya gaba daya, domin kokarin neman karin karfin samun ci gaba.

Dadin dadawa, Xi Jinping ya ce, shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar Siliki ta ruwa na karni na 21, wato shirin "Ziri daya da hanya daya" muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka bisa sabon halin da ake ciki a duk duniya domin kokarin kafa bude kofarta daga dukkan fannoni ga sauran kasashen duniya gaba daya, kuma muhimmin shiri ne da kasar Sin ta tsara domin karfafa yin hadin gwiwar tattalin arziki na shiyya-shiyya da neman ci gaba tare da sauran kasashen dake yankin baki daya.

Mr. Yasuo Fukuda, shugaban kwamitin dandalin tattaunawa na Asiya na Boao, da Mr. Shaukat Aziz, tsohon firaministan kasar Pakistan da Mr. Jean Pierre Raffarin, tsohon firaministan kasar Faransa da sauran kusoshin kwamitin sun bayar da jawabai bi da bi a gun ganawar. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China