in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar Asiya na Bo'ao
2015-03-29 20:20:12 cri
Yau Lahadi 29 ga wata da yamma, aka rufe taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar Asiya na Bo'ao a garin Bo'ao dake lardin Hainan a kudancin kasar Sin.

Mahalarta taron da suka zo daga kasashe 49 da kuma wakilan kafofin watsa labarai kusan 2786, kana wakilan da suka halarci taron sun shafi manyan fannoni da suka hada da masana'antu, ilmi, watsa labarai da dai sauransu, haka kuma an samu halartar wakilan gwamnatocin kasashen da abin ya shafa.

Bugu da kari, wasu mahalarta taron sun bayyana cewa, bayan kwanaki hudu da aka shafe ana wannan taro, sun ce sun kara saninsu game da manyan batutuwan dake shafar ci gaban Asiya, kana sun cimma ra'ayi daya kan wasu batutuwan da abin ya shafa, inda suka bayyana cewa, neman ci gaban Asiya cikin fahimtar juna da hadin gwiwa ba kawai ya dace da moriyar duk fadin nahiyar Asiya ba, har ma kuma zai taimaka wa farfadowa da bunkasuwar tattalin arzikin duniya da kuma zaman karko na yanayin siyasar kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China