Nasarar da Juventus ta samu a wannan karo ita ce ta biyu a jere kan AC Milan. Nasarar da ake ganin za ta farantawa kocin Juventus Massimiliano Allegri rai, kasancewar kusan shekara guda ke nan, da AC Milan ta sallame shi daga horas da 'yan wasan ta, bisa zargin gazawar sa.
Da yake tsokaci game da wannan nasara da 'yan wasan sa suka samu, Allegri ya ce a baya sun sha da kyar a hannun Milan, amma yanzu sun samu zarafin farfadowa.
Idan dai har Juventus ta dauki kofin Serie A na bana, zai kasance karo na 4 a jere da ta samu damar lashe kofin.
A daya hannun kuwa AC Milan, wadda ta rasa nasara a wasannin ta 4 cikin wasanni 5 da ta buga, ta sake yin kasa zuwa matsayi na 11 bayan wasannin farkon makon nan. (Saminu Alhassan)