in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa a hana kasar Tunisia shiga gasar cin kofin Afirka mai zuwa
2015-02-12 16:43:32 cri

Takaddama ta barke tsakanin hukumar gudanar da wasan kwallon kafar Afirka ta CAF da hukumar gudanar da kwallon kasar Tunisia. Hukumar ta Tunisia dai ta yi zargi cewa an yi ma ta magudi, ya yin wasan ta da Equatorial Guinea, kuma CAF ta ki amincewa ta yi afuwa game da abinda ya biyo bayan wancan wasa. A daya hannun kuma, hukumar CAF ta bayyana cewa, idan har hukumar kwallon kafar Tunisia ba ta nemi afuwar laifin da 'yan kasar ta suka aikata ba, za ta dakatar da ita, daga shiga gasar cin kofin Afirka mai zuwa.

Ya yin wasan kusa da na kusan karshe da Tunisian ta buga da Equatorial Guinea a ranar 31 ga watan Janairu dai alkalin wasan ya baiwa Equatorial Guinea fenareti sauran mintuna kadan a tashi daga wasan. Lamarin da ya baiwa Equatorial Guinea damar rama kwallo daya da aka zura mata a raga, aka kuma tashi wasan daya da daya baya. A kuma cikin karin lokaci da aka yi ne Equatorial Guinea ta kara jefa kwallo daya a zaren Tunisia, aka kuma tashi Tunusia na da kwallo 2 Equatorial Guinea na nema.

Bisa kuma wannan fenareti da ake ganin alkalin wasan ya bayar ba bisa ka'ida ba hukumar CAF ta dakatar da shi har tsawon watanni shida. A ganin Tunisia, alkalin wasan ya tabka magudi a wancan wasan, kuma ta mika wasiku biyu ga hukumar CAF, tana mai bukatar ayi bincike kan alkalin wasan, da kuma batun rashin adalcin da aka yi ma ta.

Sai dai ana daf da kammala wancan wasa, 'yan wasan Tunisia sun kewaye alkalin wasan a cikin fili, inda wasu daga cikin su suka yi yunkurin dukan shi. Kuma bayan shigar su wurin canja tufaffi dake cikin filin, 'yan wasan Tunisian sun lalata kofar dakin da kuma wani firji dake ciki. Matakin da ya sanya hukumar CAF nuna fushin ta a fili, tana mai cewa dole ne Tunisia ta biya tarar dala dubu 50, a matsayin diyya hasarar da suka haifar, tare da gabatar da bukatar neman afuwa ga CAF kafin ranar 5 ga watan nan.

Game da hakan, hukumar wasan kwallon kafar kasar ta Tunisia ta gudanar da taro a ranar 4 ga watan nan, inda ta tsaida kudurin kin neman gafara ga CAF. Kakakin hukumar ya bayyana cewa kungiyar Tunisia na kalubalantar abinda aka yi ma ta. Duk kuwa da cewa tuni CAF ta ce idan har Tunisian ta ki neman gafarar laifin da 'yan wasan ta suka aikata, mai yiwuwa ta fuskanci hukuncin dakatar da ita daga buga gasar cin kofin Afirka mai zuwa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China