150312-Yao-Ming-ya-jinjinawa-sauyin-da-kasar-Sin-ke-gudanarwa-game-da-kwallon-kafa-zainab.m4a
|
Tsohon shahararren dan wasan kwallon Kwando dan kasar Sin Yao Ming, ya ce kasar Sin na daukar matakan da suka dace, wajen bunkasa harkokin wasan kwallon kafa. Ciki hadda batun habaka wasan a makarantu, matakin da ya ce zai taimaka matuka wajen raya harkar, ta yadda a nan gaba wasu wasannin ma za su yi kishin irin nasarar da wasan na kwallon kafa zai samu a nan kasar Sin.
A cikin watan Fabarairun da ya gabata ne dai shugaban kwamitin gudanar da sauye-sauye game da harkokin wasanni na kasar Sin, kuma shugaban kasar Xi Jinping, wanda ke cikin masu sha'awar kwallon kafa, ya kaddamar da wani sabon shiri na raya kwallon kafa, harkar da ba ta samu wani babban ci gaba a kasar Sin a cikin 'yan shekarun baya bayan nan ba.
Da yake tsokaci game da matakan da aka fara dauka yanzu haka, Yao ya ce yana farin ciki da ganin yadda aka shigar da koyar da yara kanana cikin harkokin koyon wasan kwallon kafa, matakin da ya ce ya yi matukar dacewa.
"Ina fatan ganin karin matakai na aiwatar da wannan manufa, ciki hadda batun irin matakan da sassa daban daban za su dauka wajen cimma nasarar wannan kuduri" a kalaman Yao.
Ya kuma kara da cewa babban kalubalen da Sin ke fuskanta a fannin kwallon kafa shi ne nisan da harkar ta yi da makarantu, a ganin sa dukkanin harkar samar da kwararru da ta yi nisa da makarantu, ko wadanda ke cikin ta basu da ilimi, ba za a cimma nasara a cikin ta ba.
Yao ya ce yana fata harkar kwallon Kwando ma za ta samu irin wannan gata da harkar kwallon kafa ke samu a kasar Sin.(Saminu Alhassan)
Beijing: Dakunan wasannin Olympics na 2008 za su taimaka wajen karbar bakuncin gasar lokacin sanyi ta 2022.
Mamban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kuma zaunannen mamban kwamitin birnin Beijing Yang Xiaochao, ya bayyana wa 'yan jarida cewa, dakunan wasanni da aka gada daga wasannin Olympics na birnin Beijing na shekarar 2008, za su taimaka wajen samun damar karbar bakuncin gasar Olympic ta lokacin sanyi ta 2022.
Tawagar bincike ta kwamitin wasannin Olympics na duniya IOC, za ta kawo ziyara nan birnin Beijing, domin nazartar wuraren da birnin ya tanada, daga ranar 24 zuwa 28 ga watan Maris din nan. A baya dai kwamitin wasannin na Olympics dake nan birnin Beijing, ya taba bada izni ga wata hukuma domin gudanar da bincike kan yawan mutanen da suke goyon bayan neman karbar bakuncin gasar ta Olympics ta lokacin sanyi ta 2022. Kuma sakamakon kididdigar da aka samu ya nuna cewa kwatankwacin yawan mutanen dake Beijing, da gundumar Yanqing, wadanda ke nuna goyon baya ga gasar ya zarce kashi 90 cikin dari, inda adadin a birnin Zhangjiakou ya kai kashi 99 cikin dari.
Game da hakan, Yang Xiaochao ya bayyana cewa, birnin Beijing yana da fifiko, kan yawan mutanen dake nuna goyon baya game da daukar bakuncin gasar, da fasahohin gudanar da ita. Kuma idan aka cimma nasarar daukar bakuncin ta, za a bukaci kara gina dakin wasa daya kacal, yayin da za a yi amfani da sauran wadanda ake da su na gasar Olympics na lokacin zafi na Beijing.
A watan Febrairun bana ne dai tawagar bincike ta kwamitin wasannin Olympics na duniya, ta duba birnin Almaty dake kasar Kazakhstan, inda ta bayyana cewa, birnin na Almaty yana da karfi wajen daukar bakuncin gasar Olympics na lokacin sanyi wanda shi ma yake nema.
An ce, bayan da tawagar binciken ta kammala duba birnin Beijing, za ta gabatar da wani rahoto game da biranen biyu, wanda zai kasance muhimmin mataki gabanin jefa kuri'u, da tsaida birnin da za a mikawa bakuncin gasar a watan Yulin wannan shekara.(Zainab)