in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashe uku sun isa kusa da inda jirgin Jamus ya fadi
2015-03-26 11:06:47 cri
Shugaban kasar Faransa François Hollande, da shugabar gwamanatin Jamus Angela Merkel, da firaministan kasar Spaniya Mariano Rajoy, sun iso garin Seyne dake kusa da wurin da jirgin saman kasar Jamus ya fadi, inda suka saurari rahoton da jami'an yanki na gwamnatin kasar Faransa suka gabatar game da ayyukan ceto da aka gudanar.

Wasu iyalan mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin su ma sun isa yankunan dake dab da garin Seyne, domin ganawa da shugabannin kasashen uku.

Da yake tsokaci game da halin da ake ciki, shugaba Hollande ya bayyana wa taron manema labaru na hadin gwiwar shugabannin uku cewa, kasarsa za ta yi namijin kokarin tattara dukkan gawawwakin wadanda hadarin ya ritsa da su, ta kuma mika su ga iyalansu.

A nasa bangare, cikin wani jawabi da ya gabatar a birnin Paris a jiya Laraba, shugaban hukumar bincike game da tsaron jiragen saman kasar Faransa, ya ce hukumarsa ta riga ta samu abubuwan da ke ajiye cikin akwatin nadar bayanan jirgin saman.

Jirgin saman kasar ta Jamus na kamfanin Germanwings kirar "Airbus A320", ya fadi ne a yankin tsaunukan French-Alpes dake kudancin kasar Faransa, a kan hanyarsa ta zuwa birnin Dusseldorf na kasar Jamus, daga birnin Barcelona na kasar Spaniya a ranar Talata. Ya zuwa karfe 11 na safiyar jiya Laraba, an tabbata kasashen mafi yawa daga mutane da suka rasa rayukansu a sakamakon hadarin, ciki har da 'yan kasar Jamus 72, da 'yan Spain 35, da mutum 2 daga Australia. Sauran sun hada da mutane 2 daga Argentina, da 'yan Iran 2, da 'yan Venezuela 2 da kuma dan Amurka 1.

Akwai kuma sauran mutane daidaya daga kasashen Birtaniya, da Holand, da Columbia, da Mexico, da Japan, da Denmark, da Belgium, da Isra'ila, da kuma sauran wasu da ba a kai ga tabbatar da kasashensu ba tukuna. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China