in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IAEA ta ce ba ta samu karin haske ba daga Iran kan shirinta na nukiliya
2015-03-03 14:25:37 cri

Hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA ta ce, ba ta da zarafin tabbatar da wasu batutuwan da suka shafi shirin nukiliya na kasar Iran domin hukumomin Teheran ba su bayar da karin haske kan wasu bayanai ba yadda ya kamata, in ji IAEA a ranar Litini.

Ya kamata Iran ta samar da bayanai da karin haske da za su taimakawa hukumar tantance wasu ayyuka biyu da aka dakatar, in ji darekta janar na hukumar Yukiya Amano a cikin wani jawabin gabatarwa a gaban kwamitin manyan jami'ai.

An kasa tabbatar da manufar ayyukan nukiliya a Iran, in ji mista Amano. Tare da bayyana cewa, hukumarsa a shirye take wajen warware duk wasu batutuwan da ba a warware ba, ya kuma jaddada cewa, wannan shirin ba zai ci gaba haka ba. IAEA ta bukaci Iran da ta samar da bayanai kan wadannan batutuwan biyu dake kan tebur da suka shafi shirinta na nukiliya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China