Wani sabon zagayen shawarwari tsakanin manyan kasashe shida Sin, Amurka, Faransa, Ingila, Rasha da Jamus da kuma kasar Iran ya gudana a ranar Lahadi a birnin Geneva na kasar Swiss.
Wannan shi ne zagaye na biyu na shawarwarin da suka biyo bayan tattaunawar Vienna a cikin watan Nuwamban da ya gabata, inda masu shawarwarin suka amince da kara tsawaita lokaci har zuwa karshen watan Yuni domin kai ga cimma wata yarjejeniyar karshe kan nukuliya na kasar Iran. Zagayen shawarwarin na wannan karo ya kasance mai karfi, na kut da kut kuma mai zurfi, wanda kuma ya taimaka wajen fadada filin fahimtar juna, in ji Wang Qun, darektan cibiyar bincike da sa ido kan makamai na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, kana kuma shugaban tawagar kasar Sin, bayan an shafe yini guda ana tattaunawa a birnin Geneva.
Haka kuma ya bayyana cewa, dukkan bangarorin da abin ya sha sun amince wajen gudanar da wani sabon zagayen shawarwari a farkon watan Febrairu mai zuwa.
A cewar masu fashin baki game da wannan batu, an samu ci gaba kadan a cikin shawarwarin baya bayan nan, amma kuma har yanzu akwai manyan batutuwan da bangarorin biyu ba su warware ba. (Maman Ada)