in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun kolin kasar Sin ta gyara hukuncin da aka yanke kan wasu manyan laifuffuka 10 a shekarar 2014
2015-03-19 14:55:57 cri

A jiya Laraba, kotun koli ta kasar Sin ta bayar da rahoton aiki na shekarar 2014, inda aka fayyace cewa, a shekarar 2014, kotun kolin ta gyara hukuncin da aka yanke a baya kan wasu manyan laifuffuka 10 ciki har da batun Hu Gejiletu.

Rahoton ya ce, a shekarar bara, kotunan kasar Sin sun yanke hukunci kan laifuffuka da suka kai 125,273, hakan ya sa aka tabbatar da adalci wajen kare hakkin mutanen da abin ya shafa. Kana an gyara hukuncin da aka yanke a baya kan wasu laifuffukan da ake ganin ba a yi adalci ba

Rahoton ya kuma bayyana cewa, kotuna daban daban na kasar Sin suna nuna adalci a ko wane kara da aka gabatar musu, domin kiyaye hakkin jama'ar kasa bisa tsarin shari'a.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China