Bayan da aka nazarci kididdigar da M.D.D. da sojojin Amurka da hukumar kare hakkin dan Adam ta Siriya suka bayar, hukumar ta bayyana cewa, mutane kimanin dubu 76 ne suka mutu a kasar Siriya a shekarar 2014 sakamakon rikicin.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, rikicin na da alaka da kungiyar masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama. Kana rikicin da ya barke tsakanin gwamnatin Iraki da kungiyar ISIS ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 21. A kasar Afghanistan kuma, wannan adadi ya kai 14638, yayin da yawan mutanen da suka mutu a Najeriya ya kai 11529.(Bako)