in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MMD ya jaddada niyyarsa ta kare fararen hula yayin rikici
2014-02-13 14:15:03 cri

Kwamitin tsaro na MDD ya jaddada a ranar Labara niyyarsa ta kare fararen hula a lokacin barkewar yake-yake, tare da yin kira ga bangarori masu gaba da juna da su himmantu wajen amsa muhimman bukatun mutanen da yaki ya rutsa da su.

A yayin wata muhawara kan wannan batu, kwamitin tsaro ya cimma wata sanarwa, inda a cikinta ya jaddada niyyarsa ta kare fararen hula a lokacin yake-yake da daukar niyyar ganin an cigaba da aiwatar da dukkan kudurorin da suka shafi wannan batu.

Kwamitin ya amince da cewa, shi kansa da kuma kasashe mambobi na karfafa batun kare fararen hula, in ji sanarwa tare bayyana cewa, mambobin kwamitin tsaro sun nanata wajibcin tawagogin MDD dake da hurumin kare fararen hula da su tabbatar da zaman lafiya da gudanar da aikinsu yadda ya kamata, haka kuma yana da muhimmanci a ce manyan jami'an wadannan tawagogi su cigaba da rubanya kokarinsu wajen kare fararen hula.

A yayin taron, manyan jami'an MDD da dama sun bayyana a gaban mambobin kwamitin tsaro kan wannan batu.

Ina bakin cikin sanar da kwamitin cewa, duk da yawan dokokin da suka shafi 'yancin dan Adam da 'yancin ba da taimakon jin kai da kuma taimakon kafofin sadarwa na jama'a wajen farautar munanan ayyuka kan fararen hula, har yanzu ana cigaba da kashe mutane, jikkata su tare da azabatar da su a yayin da ake kai hare-hare a lokacin yake-yake, in ji mataimakiyar sakatare janar na MDD kan harkokin jin kai madam Valerie Amos tare da ba da misalin rikicin kasar Sham, Afrika ta Tsakiya da Sudan ta Kudu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China